Amurka Ta Fitarda Sabbin Sharrudda Ga Masu Shiga Kasarta Daga Kasashen Musulmi

Amurka Ta Fitarda Sabbin Sharrudda Ga Masu Shiga Kasarta Daga Kasashen Musulmi

Gwamnatin kasar Amurka ta fitar da sabbin sharudda na bada visar shiga kasar ga masu zuwa kasar daga kasashen musulmi shidda.

Kamfanin dillancin Labaran Associated Press, ya ce a jiya Laraba ce gwamnatin Donal Trump ta bada sanarwan cewa duk wadanda suke son shiga kasar Amurka daga wadan nan kasashe shidda dole ne su cika wadanda sharudda, wadanda a halin yanzu suna hannun ofisoshin jakadancin Amurka wadanda abin ya shafa.

Sharuddan suna hada da cewa masi sun shigan Amurka daga wadannan kasashe yana da iyaye, ko Matarsa, Yaya, na miji ko mace wadanda suka kai shekarun sharia, suruki, surukuwa, da kuma wasu dangi na kusa.

Labarin ya kara da cewa wadannan sharudda basu hada da kakanni, ammi, ko amma ko yayansu da kuma sauran dangi na kusa da nesa. Kasashen da abin ya shafa dai Iran, Libya, Somalia, Sudan, Syria, and Yemen.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky