Amurka ta cafke dan Libya da ake zargi da kitsa harin Bengazi

Amurka ta cafke dan Libya da ake zargi da kitsa harin Bengazi

SHUGABAN Kasar Amurka Donald Trump ya sanar da kama wani dan kasar Libya da ake zargi da kitsa harin Benghazi, da ya yi sanadiyar mutuwar Jakadan Amurka Christopher Stevens da wasu yan kasar 3 a shekarar 2012

Shugaban ya ce, shi ya bai wa zaratan sojojin kasar umurnin gudanar da binciken da ya gano mutumin da ake zargi mai suna Mustafa al-Imam, sai dai, Trump bai yi karin haske ba a game da irin rawar da wanda ake tuhumar ya taka a harin da ya harzuka Amruka.

Majiyar ta ce yanzu haka ana kan hanyar isar da mutumin da ake zargin a Amurka domin fuskantar hukunci.

Har ila yau shugaban kasar ta Amurka ya kara da cewa, ba za su taba gajiyawa ba, a kokarinsu na gano wadanda suka kitsa harin, domin gurfanar da su a gaban kotu.

Yanzu haka dai, ana yi wa wani dan kasar ta Libiya, Ahmed Abou Khattala, shari’a a birnin Washington, a kan hari, shekaru 3 bayan da wani sojan kundunbalar Amruka ya kama shi, tare da tisa keyarsa ta jirgin ruwa zuwa Amruka.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky