Amurka Na Mutunta 'Yan Afrika Sosai_ Wasikar Trump Ga AU

Amurka Na Mutunta 'Yan Afrika Sosai_ Wasikar Trump Ga AU

Shugaba Donald Trump ya bayyana a cikin wata gajeriyar wasika da ya aikewa shugabannin Afrika cewa '' Amurka tana mutunta 'yan Afrika kwarai da gaske''

Wasikar ta Trump ta ce Amurka tana mutunta  Afrika da hulda dake 'tsakaninta da kungiyar AU da mambobinta da kuma al'ummarta a  kwarai da gaske.

Trump yana mai kuma cewa a cikin wasikar, dakarun Amurka na aiki kafada da kafada dana Afrika don yaki da ta'addanci, kuma akwai hulda mai kyawo tsakanin bangarorin biyu wajen inganta harkokin kasuwanci.

An dai bayyana wannan wasika ce ga shuwagabannin Afrika dake halartar taron koli na kungiyar tarayyar Afrika karo na 30 dake gudana yanzu haka a birnin Adis Ababa na kasar Habasha.

A cikin wasikar Trump ya ce sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson zai ziyarci nahiyar ta AFrika a watan Maris.

Wannan wasikar ta Trump dai na zuwa makwanni biyu bayan kalamen cin mutunci da ya yi ga nahiyar ta Afrika, batun da ya janyo tofin Allah tsine daga shuwagabanni da bangarori daban daban na duniya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky