Amnesty: Sojojin Najeriya Sun Kashe Kauyawa 35

Amnesty: Sojojin Najeriya Sun Kashe Kauyawa 35

Kungiyar kare hakkin bil'adama din ta ce a kalla mutane 35 ne sojojin Najeriya suka kashe ta hanyar kai hari da jiragen yaki

majiyar kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta yi suka da kakkausar murya akan kisan mutanen karkarar tare da bayyana shi a matsayin wanda ya sabawa doka.

Bugu da kari, kungiyar ta ce a daruruwan mazauna karkara ne suka mutu a watannin baya amma babu wani yunkuri da gwamnatin Najeriya ta yi domin ba su kariya.

A ranar 4 ga watan Disamba na 2017 jiragen yakin kasar sun kai hari akan wani kauye a matsayin gargadin hana rikicin makiyaya da manoma a jahar Adamawa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky