Al'ummar Musulmin Amurka Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Matakin Trump Kan Qudus

Al'ummar Musulmin Amurka Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Matakin Trump Kan Qudus

Dubban musulmi a kasar Amurka sun gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da matakin da shugaban kasar Donald Trump ya dauka na shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila.

Majalisar Musulmin Amurka ta US Council of Muslim Organization ce ta shirya zanga-zangar, inda dubban al'ummar musulmin Amurka da kungiyoyin musulmi fiye da 35 suka halacci zanga-zangar suna rera taken jaddada goyon bayansu ga al'ummar Palasdinu da ake zalunta tare da daga kwalaye da suke dauke da rubuce-rubucen cewa: Trump da Natenyahu suna son kunna wutan yaki, Birnin Qudus fadar mulkin al'ummar Palasdinu ne da sauransu.

Masu zanga-zangar sun tafi har zuwa Majalisar Dokokin Kasar Amurka suna bayyana goyon bayansu ga al'ummar Palasdinu tare da neman mahukuntan kasar da su hanzarta janyewa daga mummunan matakin da shugaban kasar Donald Trump ya dauka kan birnin Qudus domin warware rikicin Palasdinawa da Yahudawa cikin adalci.

Tun a ranar 6 ga wannan wata na Disamba ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauki matakin shelanta birnin Qudus na Palasdinu a matsayin fadar mulkin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila tare da bada umurnin maida ofishin jakadancin Amurka daga Tel-Aviv zuwa birnin na Qudus lamarin da ya ke ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine daga sassa daban daban na duniya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky