Al'ummar Iran Sun Amsa Kiran Imam Khamain (r.a) Inda Suka Fito Domin Nuna Goyon Bayansu Ga Al'ummar Palastin A Ranar Qudus Ta

Al'ummar Iran Sun  Amsa Kiran Imam Khamain (r.a) Inda Suka Fito Domin  Nuna Goyon Bayansu Ga Al'ummar Palastin A Ranar Qudus Ta

Miliyoyin Iraniyawa ne suka fito zanga-zangar ranar Qudus ta duniya wanda marigayi Imam Khumain (r.a) ya assasa duk Juma'ar karshen Azumi Ramalan da kuma jaddada taken Allah wadai tare da yin tofin Allah tsine kan haramtacciyar kasar Isra'ila da manyan kasashen duniya masu girman kai da suke goya mata baya.

Kamar kowace shekara a karshen Juma'ar watan Ramalana mai alfarma; al'ummar Iran sun fito kwansu da kwarkwatansu, inda suka gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta duniya da nufin jaddada goyon bayansu ga al'ummar Palastinu da ake zalunta su na rera taken tofin Allah tsine kan yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida da kanwa uwar gami Amurka tare da jaddada bukatar kawo karshen duk wata bakar siyasar zalunci kan al'ummar Palastinu.

Har ila yau masu zanga-zangar sun yi ta rera taken neman hadin kan al'ummar musulmin duniya tare da kawo karshen duk wata siyasar bakanta sunan addinin Musulunci da wasu jama'a ke yi ta hanyar kai hare-haren ta'addanci.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky