Allah ya Yiwa Tsohon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Rasuwa

Allah ya Yiwa Tsohon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Rasuwa

A yau Asabar Allah ya yi tsohon babban sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan rasuwa.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Kofi Annan ya rasu yau Asabar a wani asibiti da ke birnin Bern na kasar Switzerland yana da shekaru 80 a duniya.

Kofi Annan wanda ya yi aiki tsawon shekaru a majalisar dinkin duniya, ya zama babban sakataren majalisar a tsakanin shekarun 1997 zuwa 2006.

Ya zama babban manzon majalisar dinkin duniya mai shiga tsakani kan rikicin Syria, daga bisani ya yi murabus sakaakon matsin lamabar da ya yi ta fuskanta domin ya murguda gaskiyar abin da yake faruwa  a kasar. Haka nan kuam ya zama babban manzon majalisar mai sanya ido kan halin da 'yan kabilar Rohingya suke ciki bayan kisan da aka yi musu a Myanmar.

Sakamakon ayyukan wanzar da sulhu da zaman lafiya da Kofi Annan ya yia  duniya, ya samu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky