Alhazai you ne daga Nageria suka rasa rayukansu a Saudiyya

Alhazai you ne daga Nageria suka rasa rayukansu a Saudiyya

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta ce alhazan kasar uku ne suka rasu a lokacin aikin hajjin bana.

Hukumar ta ce mata shida sun yi bari yayin aikin hajjin a kasa mai tsarki.

Kwamitin lafiya na hukumar ta aikin hajji - wanda ya gabatar da rahotonsa bayan kammala aikin na hajji - ya ce alhazan da suka mutu sun fito ne daga jihohin Kano da Lagos da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Wannan ce dai shekarar da aka fi samun karancin alhazan da suka mutu a aikin hajji a 'yan shekarun nan.

Kwamitin ya ce kimanin 8,571 ne suka ga likita a lokacin ibadar, sannan a yanzu haka kuma an kwantar da takwas a asibitocin kasar.

A bara dai alhazan kasar 15 ne suka mutu a kasar ta Saudiyya, yayin da a 2016 kuma adadin wadanda suka mutu ya kai 18, a cewar hukumar aikin hajjin ta Najeriya.

An fara mayar da alhazan Najeriya gida

Alhazan Najeriya sun fara koma gida bayan kammala aikin hajjin bana.

Da asubahin Litinin ne jirgin farko dauke da alhazan babban birnin tarayya Abuja su 225 ya baro filin jirgin sama na Jidda.

Bayanan da hukumar jin dadin alhazan kasar ta wallafa a shafinta na Instagram ya nuna cewa jirgi na biyu ya taso daga Jidda da wasu alhazan jihar Sakkwato 259.

Hukumar jin dadin alhazan ta Najeriya NAHCON ta ce tana fatan kammala jigilar alhazan kasar cikin makwanni uku.

Shugaban hukumar Barista Abdullahi Mukhtar ya ce a bana babu wani hadari da alhazan kasar suka fuskanta, ko wata gagarumar matsala a yayin aikin hajjin na bana.

A baya dai alhazan Najeriya kan shafe kwanaki da dama bayan kammala aikin hajji gabanin mayar da su gida, abin da a wasu lokutan har zanga-zanga suke yi a kasar ta Saudiyya domin neman mayar da su.

A bana dai yawan alhazan kasar ya ragu sosai idan aka kwatanta da shekarun baya.

'Yan Najeriya fiye da 55,000 ne suka je aikin Hajjin bana.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky