A yau Ne Nishfu Shaaban A Iran Da Iraqi

A yau Ne Nishfu Shaaban A Iran Da Iraqi

Dubban dubatan masu ziyara daga ciki da kuma wajen kasar Iraqi ne suka isa haramin Imam Husain (a) dake karbala na kasar Iraqi don raya daren haihuwar Imam Mahammad bin Hassan Al-askari (a) wato Imam Mahdi (a)

Tashar television ta al-alam ta bayyana cewa dubban daruruwan masu ziyara daga ciki da wajeb kasar Iraqi ne suka isa birnin na Karbala don raya wannan daren mai al-barka. 

Labarin ya kara da cewa gwamnatin kasar Iraqi ta tanaji jami'an tsaro isassu don tabbatar da cewa an gudanar da wannan bikin cikin zaman lafita ba tare da wani tashin hankali ba. 

A nan kasar Iran ma miliyoyin mutane ne suka ziyarci wuraren ziyara da kuma masallatayya da Husainiyoyi don raya wannan daren. A cikin bukukuwa na daren jiya dai daruruwan matasa maza da mata ne suka yi auren gamagari don neman albarkan daren na nisfi shaaban.  


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky