AWWALIYYAH DIN MANZON ALLAH (SAWA) A MUSULUNCI, WACE IRI CE? ZAMANIYYAH CE KO RUTBIYYAH?

AWWALIYYAH DIN MANZON ALLAH (SAWA) A MUSULUNCI, WACE IRI CE? ZAMANIYYAH CE KO RUTBIYYAH?

AWWALIYYAH DIN MANZON ALLAH (SAWA) A MUSULUNCI, WACE IRI CE? ZAMANIYYAH CE KO RUTBIYYAH?
__ Sheikh Hamzah Muhammad Lawal

A cigaba da tafsirin ayoyi biyar din farko na Suratul Bakara wayanda suke siffata masu tsoron Allah Subhanahu wa Ta’ala, wato Al-Muttaqeen, wayanda wayannan din ne Alkur’ani yake zama ma shiriya, wanda kuma akan wannan asasin ne Sheikh Hamzah Muhammad Lawal yace yake bincike akan Alkur’ani da Wahayi da Annabci.
Sannan a cikin wannan ne Malamin ya fara bincike kan Isma din Annabawa (as) mudlaqan ta hanyar da’awar cewa su dukkansu suna a kan As-Siradal Mustaqeem, wato hanya mikakka. Malamin yace wannan ne kuma ya sa ya dauki Ibrahim (as) yake bincike takaitacce akan shi.
A wannan zama na goma sha daya na tafsirin Alkur’ani Mai Girma a wannan watan na Ramalana wanda Sheikh Hamzah Muhammad Lawal yake gabatarwa ya bijro da wata aya a cikin Alkurani inda Allah ya umurci Manzon Allah yayi ishara ya zuwa gare ta cewa yace WA ANA AWWALUL MUSLIMIN, fadin Manzon Allah (sawa) cewa shine farkon masu mika wuya, me yake nufi? Awwaliyyah dinshi Zamaniyyah ( ta rigaya a zamani) ce ko Rutbiyyah ( ta rigaya a mukami)?
Malamin yace:
 “ Koda dan tsokaci dangane da wannan ayar An’am din domin mu nuni ga cewa wannan Awwaliyyah din da Allah Suhbanahu wa Ta’ala ya umurci Manzon Allah (sawa) da yayi masu ishara ya zuwa gare ta, wacce irin Awwaliyyah ce?- Bamu da lokacin, ba wai ina so ne ya zama nayi tafsirin ayoyin ba. Kawai ishara ‘aabira’ ya zuwa ga fifikon daraja na Manzon Allah (sawa) akan dukkan halittu da dukkan yan Adam har da ULUL AZMI dinsu daga cikin Manzanni. Allah Ta’ala yana ce mashi a wani wuri ya daure KAMA SABARA ULUL AZMI MINAR RUSULI, yana cewa Manzon Allah (sawa) Ka daure kaman yanda Ulul Azmi daga cikin Manzanni suka daure, yana nufin kenan kai ma kana cikinsu. Ka daure kamansu me yake nufi? Kana cikinsu.
 “ To, amma Allah bai ambaci su wane ne Ulul Azmi ba a waccan ayar, sai ya zo ya ambace su a Ahzab da Shura kaman yanda muka nuna maku. To, sannan kuma sai ya tsame Manzon Allah (sawa) a cikinsu din ya ambace shi a gabansu ba tare da kiyaye tartibin abkuwa a zamani kaman yanda muka nuna. To, sannan kuma sai a nan gun kuma yake cewa yace masu nine Farkon wanda ya mika wuya, QUL INNA SALATIY WA NUSUKIY WA MAHYAYA WA MAMATIY LILLAHI RABBIL ALAMIN, Ka ce masu hakika sallah ta da nusuk dina da rayuwata da mutuwata duka na Allah ne Subhanahu wa Ta’ala.. har zuwa inda yake cewa WA ANA AWWALUL MUSLIMIN, kuma nine farkon wayanda suka mika wuya.
 “ Nan da yake cewa WANA AWWALUL MUSLIMIN, inji Allama Tabataba’I shine cewa akwai dalili akan cewa Shi Manzon Allah (sawa) shine farkon mutane gabaki daya ta bangaren darajar musulunci, wato darajar mika wuya da matsayin musulunci din. Shi yasa suke cewa wannan Awwaliyyah din ta wannan ayar Awwaliyyah ce Rutbiyyah, ba Awwaliyyah ce Zamaniyyah ba. Awwaliyyah ce ta rutba, wato ‘rank’ na wujud, na hakika na ma’ana.”
Malamin ya kara da cewa da ce Awwaliyyah din Zamaniyyah ce da ba zai yiwu ba wasu gungu na musulmi su rigaye shi a zamani ba.
 “ Gabanin Manzon Allah (sawa) ai akwai zamani na wasunshi wayanda suka mika wuya. To, in a zamani ake nufi, in ayar zamani take nufi ai ma’anarta ba zata mike ba kenan. Kuma hakika Allah Subhanahu wa Ta’ala ya hikaito wannan dangane da Nuh (as) lokacin da yake cewa WA UMIRTU AN AKUNA MINAL MUSLIMIN, kuma an umurce da in kasance da cikin wayanda suka mika wuya, Suratul Yunus, aya 72. Kuma an hikaito wannan daga Annabi Ibrahim a fadin Allah Azza wa Jalla cewa …..ASLAMTU LI RABBIL ALAMIN, na mika wuya ga Ubangijin Talikai, kuma ya riga Manzon Allah (sawa) zuwa bayan Nuh (as), Suratul Bakara, aya 131. Kuma an naqalto wannan daga shi da kuma danshi Isma’il (as) inda suke cewa RABBANA WAJ’ALNA MUSLIMAINI LAKA, Ya Ubangiji kuma ka sanya mu mu biyu masu mika wuya ya zuwa gare ka, Al-Bakara, 128.
 “ Kuma Allah ya hikaito wannan dangane da Lud (as) a fadinshi FAMA WAJADNA FIHA GAIRA BAITIN MINAL MUSLIMIN, Bamu samu ba a cikin garin koma bayan gida daya daga cikin masu mika wuya, wato gida daya ne suka musulunta, Az-Zariyyat, aya ta 36. Kuma Allah Ta’ala ya hikaito Sarauniyyar Saba’ inda yake cewa WA UTINAL ILMA MIN QABLIHA WA KUNNA MUSLIMIN, kuma mun kasance musulmi masu mika wuya, a Suratun Namli, aya ta 42. In abinda take nufi yana nufin mika wuya ga Allah Kenan. Sannan akwai shi a fadinta cewa WA ASLAMTU MA’A SULAIMANA LILLAHI RABBIL ALAMIN, kuma na mika wuya tare da Sulaiman ya zuwa ga Allah Subhanahu wa Ta’ala Ubangijin Talikai, Suratun Namli, aya ta 42.
 “ Saboda haka akwai wayanda suka mika wuya ga Allah a zamunnan da suka zo kafin zamanin Manzon Allah (sawa). Kenan me yake nufi da nine farkon wanda ya mika wuya? Kuma babu wanda aka siffata da wannan a Alkur’ani da kasantuwa farkon wanda ya mika wuya in banda abinda ke cikin wannan ayar ta An’am inda Allah Ta’ala ya umurce Manzon Allah (sawa) akan cewa ya gayawa mutanenshi shine farkon wanda ya mika wuya. Babu wani wuri in banda wannan, sai abinda yake cikin Suratuz Zumar na fadin shi Manzon Allah (sawa) din cewa QUL INNI UMURTU AN A’ABUDALLAHA MUKHLISAN LAHUD DIN WA UMURTU LI AN AKUNA AWWALAL MUSLIMIN, Kace- shima talqini ne a wurin- Hakika an umurce ni in bautawa Allah ina mai tsarkake addinin ya zuwa gare shi kuma an umurce ni da cewa in kasance farkon wanda ya mika wuya. To, Kenan, me yake nufi da wannan? Kila an ce inji Al-Allamah; kila abinda ake nufi shine nine farkon wanda ya mika wuya a cikin wannan al’ummar da dalilin cewa saboda Ibrahim (as) ai shine farkon wanda ya mika wuya, saboda haka duk wanda ya zo bayan Ibrahim yana bibiyanshi ne a cikin mika wuya. Wani zai iya cewa haka, wato ai ana nufin cewa Manzon Allah shine farkon wanda ya mika wuya a cikin al’ummarshi saboda Ibrahim ya riga shi shine ma ya sanya mana suna musulmi, saboda haka duk wanda ya zo bayan Ibrahim (as) yana binshi ne.
 “ To, raddin wannan ishkal din inji Allamah shine wannan qayyadewa da cewa farkon wanda ya mika wuya a cikin al’ummarmu wannan babu dalili akanshi. Ayar Mudlaqa ce, babu dalili akan Taqyidin. To, wannan kuma cewa Ibrahim shine farkon wanda ya mika wuya ya musulunta, duk wanda ya zo a bayanshi yake, da wayancan ayoyin da muka Ambato sun tunkude wannan, Kaman Nuh (as) inda yake cewa an umurce shi da ya kasance daga cikin musulmi kuma ya riga Ibrahim (as). Saboda haka wannan ba dalili bane. Lokacin da Allah Ta’ala ya umurce ManzonShi (sawa) akan ya kasance farkon wanda ya mika wuya abinda yake nufi shine cewa AWWALIYYAH RUTBIYYAH, ba AWWALIYYAH ZAMANIYYAH ba. Shine farkon wanda ya mika wuya ga Allah Subhanahu wa Ta’ala mudlaqan.”


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky