Riwaya ta kasu kashi biyu;Ar-Riwaya Ash-Shafawiyyah da At-Tahririyyah

Riwaya ta kasu kashi biyu;Ar-Riwaya Ash-Shafawiyyah da At-Tahririyyah

In ji Sheikh Hamzah Muhammad Lawal

A cigaban darussan da Sheikh Hamzah Muhammad Lawal yake gabatarwa na Al-Milal wan Nihal da Fiqhu a duk ranar juma’a a makarantar sa dake garin Kaduna,a wannan juma’ar da ta gabata Sheikh Hamzah Lawal ya fara wani bahasi mai cin gashin kanshi wanda zai yi bincike akan Al-Mashayikhuth thalatha (shehunnai guda uku) wa’yanda suka tattara hadisan shi’a.
A cikin wannan bahasin Malamin ya bayyana cewa:
“Musulmin larabawa suna da hanyoyin guda biyu ne a wajen rawaito hadisai daga Manzon Allah(Sawa),sune;riwaya ta fatar baki(Arriwaya Ash Shafawiyyah),da riwaya ta tantacewa wato rubutawa(Arriwaya At-Tahririyyah).”
Sheikh yace ;Ar-Riwaya Ash-Shafawiyyah itace wannan yanayin sananne wajen daukan thaqafa sannan su isar da ita gaba.Riwayar shi’ir-wa’yannan wakokin da suke a wancan lokacin zamanin jahiliyyah-a lokacin jahiliyyah da farkon musulunci sune mafi bayyana daga cikin misalan wannan.Wato da baki suke yi.
Sannan ginshikan Arriwaya Ash-Shafawiyya sune “Assima’u” wato ji da kuma “Hifz” wato kiyayewa.Wato jin hadisin daga wanda yake fadi,sannan sai ka kiyaye shi sannan a dinga dawo wa dashi daga zucciya ko daga kwalkwalwan.
Sannan ya kara da cewa tunda sunnar Annabi ko ma’asum ba magana bace kawai,akwai aikinshi da tabbatarwan shi,kuma ba jin su ake ba,shedar su ake yi,to,sai ya zama shedan aikin ko tabbatarwan sai ya tsaya a matsayin ji(Assima’u).
Ya bada misali dangane da ji ko shedar riwaya daga Annabi da cewa duk lokacin da ka ji mai riwaya yace “na ji Manzon Allah yana cewa ko yace kaza…” wannan yana nuna ma cewa Manzon Allah magana yayi sannan yana hikaito maka maganar Annabi din ne.Sannan idan mai riwaya yana so ya bada labarin aiki ko taqrir din Annabi cewa zai yi “na ga Manzon Allah (sawa) yana aikata kaza…,ko kuma na ga Manzon Allah yana tabbatar da wane akan aiki kaza…”
Saboda haka,Idan Ar-Raawil Awwal yayi amfani da “his” din shi na ji ko gani ko fahimtar shi ya shedi wani abu daga  Annabi sai a ce yayi riwaya “shafawiyan”.Amma idan (Ar-Raawil Awwal) yana so ya isar da ita zuwa ga wani-bayan ya sheda yayi haml da tahammul,to,a nan wurin tana bugatan magana ko “naql” da fatan baki,sai yace misali “SAMI’ITU RASULULLAH ko RA’AITU RASULULLAH”.Wannan itace ake ce ma Ar-Riwaya Ash-Shafawiyyah.
Malamin yace hanya ta biyu ta riwaya itace;Ar-Riwaya At-Tahririyyah,wato riwaya ta rubutu.Abinda ake nufi da Ar-Riwaya At-Tahririyyah shine mai riwaya din ya rubuta zantukan Manzon Allah da ayyukanshi da ababen da ya tabbatar a littafi,wato ya rawaito tahriran,tadwinan.
Wannan rubutu da mai riwaya yayi na sunnan Manzon Allah(sawa) din shima ana ce mashi “haml”,wato ya dauki sunnah.
Shi wanda ya rubuta sunnah din wato “haamil” din in yana so ya isar da ita ya zuwa ga waninshi,to,wani lokaci zai isar da ita ne ta hanyar fatar baki(wato Shafawiyyah),wani lokaci kuma zai iya bayar da abinda ya rubuta,wannan shi ake ce ma “munawala”.Wani lokaci kuma zai iya zama “qira’atan alash sheikh” ko “qira’atan minash sheikh”,wato wani lokaci sheikh din ne yake karanta abinda ya rubuta,wani lokaci kuma kai zaka zo da abinda ka rubuta kana karantawa yana maka gyara a inda kayi kuskure,ko kuma yayi mashi kofi,ko kuma ya bashi ya je yayi kofi ya dawo mashi da shi.
Malamin yayi bayanai masu yawa a cikin wannan karatu dangane da riwaya da hadisi a wajen ‘yan shi’a,mai sha’awan cikakken bayanin zai iya neman karatun Sheikh Hamzah na Fiqhu na juma’ar da ta gabata wato 25 ga watan Agustus 2017


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky