MENENE WANNAN AL’AMARIN DA ALLAH SUBHANAHU WA TA’ALA YACE “ATA AMRULLAHI FALA TASTA’AJILUH” ? na 3

MENENE WANNAN  AL’AMARIN DA ALLAH SUBHANAHU WA TA’ALA YACE “ATA AMRULLAHI FALA TASTA’AJILUH” ? na 3

Na Maulana Al-Mujahid Sheikh Hamzah Muhammad Lawal
Yusuf Sulaiman ne ya rubuta maku.


As-Shaikud Dusiy yake cewa yanda zaka yi a gane ko kuma yanda za a hada riwayoyin don a gane shine,idan sun inganta irin wadannan riwayoyin,-saboda shi Shaikh ya san riwayoyin gabaki dayan su kuma yayi jaula a cikin su,yayi bahasosi masu yawa a cikinsu  shi yasa ya rubuta littafin Kitab Al-Gaiba.
Shine sai muce(Shaikh):shekarun shi sune shekarun shi-ka ga yanda ake jam’I tsakanin riwayoyi-amma zai bayyana ma mutane a suran saurayi  wanda yake  cikin gungun ‘yan shekara arba’in,ko kuma abin da ya kusanci shekara arba’in.
In ka ganshi ba zaka dauka cewa shekarunshi 1000 ko dubbai ko “ila akhirih”,zaka ganshi mutum dan shekara 30,35 ko 40.Ba yana nufin shekarunshi 40 bane,a’a zai bayyana a matsayin dan shekara 40.
Abinda yake karfafa wannan ta’awilin da muka yi-in ji Ash-Shaikhud Dusiy-shine daga Al-Imamus Sadiq yana cewa: “hakika Waliyullah wato waliyin Allah(daga cikin sunayen Al-Imamul Hujjah) za a rayar dashi shekarun Ibrahim Al-Khalil (as),shekara 120,amma zai bayyana a suran saurayi kammalalle(wato rashid) dan shekara 30”.Kaman Yusuf (as) misali.Shekara 120 za ta iya zama kowacce irin dattijo.Amma zai bayyana a suran dan shekara 30,mutum rashid cikakke kammalalle.
Kuma an rawaito har yanzu daga Ibn Hamman din,daga Hasan Ibn Ali,har zuwa Abi Basir,daga Abi Basir daga Imam Sadiq (as) yana cewa : “In da a ce mai tsayawa(Al-Qa’im) zai bayyana,da zai fito da mutane sunyi inkarin shi,zai dawo,zai koma masu a matsayin saurayi rashid kammalalle,saboda haka babu wanda zai iya tabbata dashi ,ko tsaya dashi a lokacin saboda yarintarshi-saboda an basu labarin cewa ga tun lokacin da aka haife shi-sai kowanne mu’umini wanda Allah Ya dauki alkawarinshi tun zarran farko”.Komai a lissafe yake a wajen Allah.
Yana da kyau ku dinga jin wa’yannan hadisan,saboda suna karawa mutum imani da kuma natsuwa,da samun karin bayanai.Riwayoyin mu akan Al-Imamul Mahdi sun fi na Ahlus-Sunnah wal Jama’a bayani akan tafsil,banda asali na Manzon Allah (sawa),to,A’immah sun kara sharhi da yawan gaske,daga gare shi dab’an,tunda a  gidan suke.Saboda haka riwayoyin Imam Mahdi daga A’immah in ka sansu kuma in kai ahlin ka sansu ne,kana iya sawwala shi Alaihis Salam,zaka iya sawwala abubuwan da zai yi duk da yake ba za a iya sanin komai da komai ba sai ya zo din.Shi kanshi asirin gaiban,hikiman gaiba,gaba daya ma’anarta,me yasa yai gaiba?yanzu mun san wasu daga cikin dalilai ko hikimomi,amma ba gabaki dayansu ba.
A wani labari  daban ya zo cewa: “A cikin Sahibuz Zaman akwai kama da Yunus(as)-yayi kama da Annabawa da yawa,zamu fada wasu,a nan an kwatanta shi da Yunus.Kun san Yunus(as) Allah kaman Ya rayar dashi sabuwa,ya aike shi sabon aike zuwa dubu dari ko abinda yayi kama da haka.WA INNA YUNUSA LA MINAL MURSALIN, IZ ABAQA ILAL FULKIL MASH’HUN,wato a lokacin da ya gudu ya zuwa ga jirgi wanda yake cike(“mash’hun” ma’anarshi cike,wato ya nauyaya),daga karshe Allah Ya ladabtar dashi kifi ya hadiye shi alhali yana abin zargi.Da ba don ya kasance yana daga cikin masu tasbihi ba,LALABISA FI BADNIHI ILA YAUMI YUB’ASUN.To sai kifin ya zo bakin gaba ya  tofar dashi bayan ya roki Allah ya tuba.Sai Allah Ya tsirar akanshi da bishiya daga Yakdin,sannan sai ya aike shi ya zuwa ga dubu dari ko fiye da haka.Wannan ba shine bahsin ba,ba tafsirin ayoyin bane,cewa yanzu an sabunta shi.
Akwai kama da Yunus (as).Dawowan shi (Yunus) daga gaibarshi  da wato kenan ganiyyar samartaka.Sun yi kama da Yunus a wannan bangaren.
Sannan akwai sauran Annabawa da yayi kama dasu,zamu yi magana akansu,ka gane cewa al’amarin shi ba ya keta al’ada bane.Ko da ya keta al’ada bai keta hankali ba balle ma bai keta al’ada din ba.
Kuma Hakika an rawaito daga Al-Imam Sadiq yace :Me kuke inkari –wato abin mamaki ne ya zama kuna inkari,kaman kuna inkarin kuduran Allah Subhanahu wa Ta’ala ko kuma abin bai afku ba –akan cewa Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya tsawaitawa ma’abucin wannan al’amarin a shekaru kaman yanda ya tsawaitawa Nuh(as) a shekau.
Aka ce,Nuh muddan sakonshi shekara 950,ba muddar rayuwarshi a doron kasa ba.Menene a ciki?
Sai Ash-Sheikhud Dusiy yake cewa: “Ko da ma a ce wadannan riwayoyin basu zo ba,a hankalce a dauka cewa kwata kwata babu wadannan riwayoyin da suke bayanin cewa zai yiwu ya rayu wadannan shekarun,da zai zama Allah zai iya.Tambaya ce akan Allah zai iya ko ba zai iya ba.A hankalce Allah zai iya ba tare da an samu sabani a cikin al’umma.In ka tambaya Allah zai iya ?ba wai cewa yayi ba,sai a ce maka zai iya saboda Allah  ALA KULLI SHAI’IN KADIR.
Wadanda zasu saba kawai sune “munajjamun” kaman yanda yake cewa.Dukkan ma’abuta shari’a (ba musulunci kawai ba)sun tafi akan halacci da ma’anar yiwuwan haka wato Allah zai iya haka .288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky