KAFIRCIN DUNIYA YA SALLADU AKAN AL’UMMAR MUSULMI NE SABODA WATSI DA (MUSULMI) SUKA YI DA KARANTARWAN ANNABI(SAWA) ( 1)

KAFIRCIN DUNIYA YA SALLADU AKAN AL’UMMAR MUSULMI NE SABODA WATSI DA (MUSULMI) SUKA YI DA KARANTARWAN ANNABI(SAWA)  ( 1)

_______Sheikh Hamzah Muhammad Lawal
Yusuf Sulaiman ya rubuto maku

Ina wa’yannan karantarwan (na Annabi) ina rayuwarmu a yanzu? Ina wannan karantarwan ta Annabi (sawa)? Da addinin da ya zo dashi, da sakon da ya zo dashi daga Allah Subhanahu wa Ta’ala, da kuma rayuwarmu a yanzu?
Rayuwa ta barna, da facaka, da alfahari, da gasa, da jabbiranci, da dagutanci, da girman kai da mamakin kai, da watsar da addini, da daukan Alkur’ani a matsayin abin kauracewa – YA RABBI INNA QAUMIK TAKAZU HAZAL QUR’ANA MAHJURA, Ya Ubangijina hakika mutane na sun dauki wannan Alkur’anin a matsayin abin yi ma hijira abin kauracewa mawa.
Su Al’ummar musulmi a janibinsu sun saki Alkur’ani, sun saki sunnan Manzon Allah (sawa), sun saki dukkan karantarwan shi gabaki daya, saboda haka suka zama kaskankantun kaskantattu a doron kasa. Su kuma kafirai suka salladu akan musulmi, ya zama suna kwallo dasu yanda suka ga dama, saboda shugabannin musulmi sun watsar da karantarwan addininsu sun koma suna sha’awar karantarwan addinin Shedan.
Wa’yanda suka tsaya a kan suna so su bi karantarwan addinin Musulunci ta asali ana sanya masu sunaye. Sun zama sune baki a cikin duniya, sun zama sune ababen yi ma isgili da dariya, sun zama sune wa’yanda aka dauka ci bayayyu. Sannan kari a kan wannan shine wa’yanda suke jahilai a cikin addinin da sunan addini din suna kara bata fuskan addinin a cikin duniya gabaki daya; wani lokaci ta hanyar ta’addanci, wani lokaci ta hanyar su’in tasarrufi, wato mummunan tasarrufi, wani lokaci ta wasu hanyoyi daban, har ya zama Kaman yanda wasu suke fadi kuma fadinsu ya zama gaskiya.
Wasu jahilai a cikin addinin musulunci sun yi ‘hijacking’ musuluncin daga hannayen musulmi na hakika na asali, wato sun kwace addinin Musulunci daga hannun musulmi na hakika. Wannan ya baiwa makiya addinin da yawa samun hanya ya zuwa ga salladuwa akan shi addinin da kuma ma’abutan shi.
Tun daga shekara dari da suka wuce a lokacin yakin duniya na daya har zuwa yau dinka din nan labarin daya ne in ban da nan da can, nadiran sosai, cewa musulmi sune kaskantattu. Tun lokacin shela wadda yanzu a rayuwar siyasa ta duniya ake ce ma “Shelar Balfour” wato “Balfour Declaration” ta 2 ga watan Nuwamba 1917, har zuwa yau labarin iri daya ne Kaman yanda nake cewa.
Shelar Balfour, itace wasika- shelar wasika ce- wadda ministan harkokin kasashen waje na Ingila a lokacin wanda ake ce ma shi Arthur James Balfour ya rubutawa wani kasurgumin Bayahude a Ingila wanda ake mashi Lord Rothschild wadda a cikin wasikar ya rubuta cewa:
“Gwamnatin Birtaniyya ta yanke a kan cewa ya kamata a samar a cikin Palasdin ‘a national home for the jews’ a samu wurin zama a matsayin kasa ma Yahudawa. Sannan kuma zasu yi duk abinda zai yiwu domin haqqaqar da wannnan”.
Wannan wasikar ita ake ce ma Balfour Declaration, jinginawa zuwa ga sunan shi ministan harkokin waje din wanda shi ya rubuta wasikar, ana ce mashi Authur James Balfour. Har zuwa 1948 har zuwa yau dinka din nan, shekara 100. Kwanan nan mutanen Palasdin suka yi bikin cikan shekara 100 na Shelar Balfour wadda wannan ranar suke ce ma ‘Ranar Masifa’ wato ‘Naqba’ ‘catastrophe’. Kila kun ji Sayyid Hasan Nasrullah kwanan nan yana cewa shelar Trump ta cewa Qudus itace babban birnin Isra’il ita tana a matsayin Balfour na biyu, kuma ta zo exactly shekara dari bayan waccan Balfour din. Ya kamata ku dinga sanin abubuwan da suke faruwa.
Idan wancan shelar ta farko wasika ce, to, wannan shelar ta biyu ita kuma “qarar” ne wanda shi Trump ya dauka saboda wauta da jahilci da rashin sanin tarihin duniya da al’ummu a cikin wannan duniyar. Wadda wannan shelar da Trump yayi tana da muhimmancin gasken gaske da kuma faranta rai saboda dalilan da zan kawo in Allah Ya yarda a wannan zaman.
Kun sani a kan cewa kafin zuwan Trump da karban shi ragamar mulki da matakan iko a Hadaddun Jihohin Amurka (United State of America) wato “Al-Wilayatul Muttahidal Amerikiyyah”. Kafin zuwan shi nan wurin, kafin karban madafan iko, dukkan shugabannin kasar Amerika suna da wannan hanqoron, kuma hakika Kaman shekara 20 da suka wuce majalisar dokoki ta Amerika din ta riga ta zartar akan cewa Qudus itace babban birnin Isra’ila, kuma tana sauraren Shugabannin kasar Amerika su aiwatar da wannan, bayan kowane wata 6 su yi ‘review’. An yi review din wannan kudurin ya kai sau 40 nake jin bayan shekara 20, wato shugaban kasan Amerika da ya iya samun wannan kumaji da karfin halin yai haka, saboda haka bayan kowane wata 6 sai yai ‘deferring’.
Wata 6 sun cika, Trump bai yi deferring ba. Mai bin labarum siyasar duniya, tun a lokacin aka fara tsammanin zai fadi wannan saboda alkawari ne na kamfen wanda yayi. (Trump) yayi alkawari lokacin kamfen cewa zai mai da birnin Isra’ila daga Tel’aviv ya mai dashi Qudus. Wannan abin da yayi cika wannan alkawarin da yayi kamfen. Ya dauka cewa duniya zata zauna ba zata tashi ba, saboda haka ‘is learning on the job’ a hankali a hankali.

Akwai cigaba…


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky