HAIHUWAN IMAM ALI(AS) A 13 GA WATAN RAJAB.Kashi na 1

HAIHUWAN IMAM ALI(AS) A 13 GA WATAN RAJAB.Kashi na 1

Na Maulana Sheikh Hamzah Muhammad Lawal(ama).
Yusuf Sulaiman ya rubuta maku

A’uzu billahi minash Shaidanir Rajeem.
Bismillahir Rahmanir Raheem.
Wasallallahu ala Muhammadin wa Alihid Dayyibinad Dahireen.Allahumma Salli ala Muhammad wa Ali Muhammad.
Imam Ali (as) zaka iya cewa tanadi ne,wato “I’idad”, “Al-I’idad An-Nabawiy” ko kuma “Al-I’idad Al-Ilahiy” in ka so kace.Tanadi ne na Manzon Allah(sawa) ko kuma a asali tanadi na Allah (T) domin daukan nauyin risala bayan shudewan Manzon Allah(sawa) daga wannan duniyar  ta zahiri da imkan.
Wannan ba karamin nauyi bane wanda Allah (T) ya dora mashi,wanda kuma yana bugatan gayan taimako daga Allah Subhanahu wa Ta’ala din,wanda kuma Allah din yayi mashi wannan taimakon.Ya zama kaman Manzon Allah Sallallahu alaihi wa Alihi wa Sallam a siffofi idan ka cire Annabci da saukan wahayi,sai ya zama abinda Manzon Allah(sawa) ya samu albarkacin wannan Annabci din,da saukan wahayi,sai ya zama da wasidan shi ya gadarwa Imam Ali(as),ba gado na zahiri ba kaman yanda zamu gani In sha Allah.
Ayatullah Al-Mirzat Tabriziy daga cikin malaman Al-Imam Al-Khomainiy wa’yanda muka sha yin ishara ya zuwa gare su yana cewa a cikin littafinshi “Al-Muraqabat”:
“Kuma ana iya sanin dalilin girmama sha uku ga watan Rajab ta fuskacin cewa wannan yinin shine yinin haihuwar cikamakin Auliyyah wanda ya rufe kofar wilaya “alal idlaq”-wa’yannan “madamin “din ban da lokacin yin bayanin su kaman yanda aka sani a cikin awa daya awa biyu alhali abinda muke so mu tattauna yana da yawa sosai.Babu lokacin yin bayanin wa’yannan “madamin” din masu yawa.
“…wannan itace ranar da aka haifi cikamakin waliyai kuma shugaban wasiyyai ,dan uwan Manzon Allah (sawa),kuma mijin Al-Batul Az-Zahra (as),ran nan ne aka haifi takobin Allah Subhanahu wa Ta’ala zararre,Amirul Mu’umin Alaihis Salatu was Salam.
“Domin haqiqa wannan yinin a cikin hukuncin hankali tabbas yana da sha’ani daga cikin sha’ani wanda yake bayani ba zai iya bayanin sha’anin dake cikin wannan yinin ba,sannan kuma harshe zai gajiya a wurin iya bayanin sha’anin wannan yinin.Domin haqqin lokuta da ranaku da kuma sha’anonin lokuta da ranaku din,ana iya kimanta su ne kawai daidai gwargwardon abinda yake afkuwa a cikinsu na daga “aldaf”din Allah Subhanahu wa Ta’ala-in ba haka ba kaman yanda muka sha fadi cewa dukkan zamuna gabaki dayansu daidai ne,ba wani bambamci tsakanin wani yanki na zamani da wani yanki saidai “hadas” din da yake afkuwa a cikinsu .
Abinda yake bambamta wannan yankin da wannan shine abinda ya afku koma bayan wancan.Kima da hakkin lokuta da ranaku da sha’anoninsu,wa’yannan din suna kimantuwa ne daidai gwargwadon abinda yake afkuwa a cikinsu na “aldaf”  da “fuyudat” din Allah Subhanahu wa Ta’ala ,wato abubuwan da suke saukowa na daga rahamomi da kudurori  a cikin wannan yanki na zamunnan.
Saboda haka daidai gwargwadon kiman da ya sauka a wannan lokacin daidai gwargwardon abinda yake bambamta wannan lokacin da sauran lokuta.To,haihuwan Ali(as) a 13 ga watan Rajab ba karami bane daga cikin “aldaf” na Allah Azza wa Jal saboda haka shine ya ba wannan ranar wannan kimar.
“….domin abinda ya bayyana a wannan yinin,da kuma abinda ya sauka a doron kasa na daga hasken wilaya din cikamakin waliyai  wanda wannan (Ali (as) din ) shine sharadin imani da kuma ginshikin imani din,kai shine ma ruhin imani,shine ran imani,wannan wanda yake kaman shine juzu’I na karshe ga sababi cikakke na daga imani da musulunci.
Abinda ya sauka a wannan yinin na wa’yannan abubuwan da muka siffata wata irin ni’ima ce wadda take wa’yannan kwakwalen na mu ba zasu iya kimanta ta ba,domin su kwakwalen ba sa iya faifaye abinda Allah Ta’ala ya tanadar da mazowa waliyya ga waliyyan Allah da imani na daga haske da karama da darajojin kusanci……”
Sannan abinda yasa wannan yinin yake da wannan muhimmancin  shine:
  “Da ba don takobin Amirul Mu’umin Imam Ali(as) ba a cikin rayuwar musulunci gabaki daya-alhali ya taimaki musulunci da takobinshi Zulfiqar –da mazowa kafirci sun karar da musulmi gabaki daya,kuma da ba a samu mataimaki da ginshiki ga musulunci ba.
Tuna,misali,da abinda ya aikata ranar Badar da ranar Hunain,kuma kayi tunani ka tsaya kayi tafukkur a fadin Manzon Allah (sawa) mai gaskiya Amintacce a ranar Kandaq lokacin da Manzon Allah yake cewa:
  “BARAZAL ISLAMU KULLUHU ILAL KUFRI KULLIHI”
Ma’ana;Musulunci gabaki dayanshi yayi fito na fito da kafirci gabaki dayanshi .
Ali (as) shine musulunci gabaki dayanshi,wa’yannan mayakan da suka zo Kandaq domin su yaki Annabi sune kafirci gabaki dayanshi.A lokacin da suna cika baki suna kirari,kowa yana tsoro Imam Ali ya tashi har sau uku sai Manzon Allah yai mashi izini.Da ya fita zai tafi sai Manzon Allah yake ce mashi : “BARAZAL ISLAMU KULLUH ILAL KUFRI KULLIHI”.
“…muce maka a takaice falalolin Imam Ali (as),masoyi ya boye su domin takiyya,sannan makiyi ya boye saboda hassada da gaba da bakin ciki,amma duk da haka sai ya zama cewa tsakanin wannan da wancan din falalolinshi sun fito sun cika sassa gabaki daya.Duk da yanda akai kokarin a boye falalolinshi din sai ya zama basu boyu ba ga kowa da kowa,ba ‘yan shi’a kawai ba,kaman yanda zamu gani kila a gaba insha Allah.
“Imam Ali shine labari mai girma wanda ake tambayo akanshi (AMMA YATASA’ALUN,ANIN NABA’IL AZIM,ALLAZI FI HIM MUKHTALIFUN),shine hanya mikakka(SIRADAL MUSTAQEEM),shine Al-Kur’ani mai karimci,shine Al-Kur’anun Nadiq,shine limamin musulmi,shugaban mu’uminai,shine wasiyyin jakadan Ubangijin Talikai –kaman yanda kake karantawa a Ramadan a Du’a’ul Iftitah ko kuma zaka karanta insha Allah-Kuma shine hasken Allah mabayyani,shine kofar Hidda (wato kofar gafarar zunubi) ,shine kofar sayyar da zunubai da neman gafarar Ubangijin Talikai,shine gefen Allah a cikin halittarshi,shine fuskarshi a cikin waliyyanshi gabaki daya (AINA WAJHULLAHIL  LAZIY YATAWAJJAHU ILAIHI…kaman yanda kake karantawa a Du’a’un Nudba).Shine wa’yannan .


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky