HAIHUWAN IMAM ALI(AS) A 13 GA WATAN RAJAB.(4)

 HAIHUWAN IMAM ALI(AS) A 13 GA WATAN RAJAB.(4)

Na Maulana Sheikh Hamzah Muhammad Lawal(ama)
Yusuf Sulaiman ya rubutu maku
..Cigaba.

Ayatullahi Sanad ya cigaba da tafsirin ayan SUMMA AURASNAL KITABAL LAZINAS DAFAINA…da cewa:
“….amma inda aka kasa ayan a karshe in da yake cewa FA MINHUM ZALIMUN LI NAFSIHI,WA MIN HUM MUQTASIDUN,WA MINHUM SABIQUN….wato daga cikinsu akwai azzulumi,daga cikinsu akwai madaidaici,daga cikinsu akwai marigayi wato wanda ya riga-
Kana iya cewa in an zabe su,to, me yasa aka kasa su kashi uku?ka samu ishtibah.Ba su AL-MUSDAFAUN din ne aka kasa uku ba,a’a,IBADUNA dinne aka kasa uku.E,gaskiya ne AL-MUSDAFAUN suna daga cikin IBADUNA,sune wa’yannan AS-SABIQUN din.Wa’yanda aka kasa ba sune AL-MUSDAFAUN ba.
“Al-Maqsamur Ra’isiy” shine IBADUNA,ba AL-MUSDAFAUN ba,wanda aka kasa shine wa?Damirin na komawa ne ya zuwa ga wa’yanda suka rigaya.Da yake cewa ….ALLAZINAS DAFAINA MIN IBADINA …. “min” din “TAB’IDIYYAH” ce wanda ta kasa IBADUNA din zuwa sassa daban daban.To shine yayi tafsirin MIN IBADUNA din,yace FA MINHUM ZALIMUN LI NAFSIHI WA MINHUM MUQTASIDUN(ay min ibadina) WA MINHUM SABIQUN BIL KHAIRAT(sune Al-musdafaun daga cikin IBAD).
  “Su “ibaduna” wato bayinmu sun kasu ne ya zuwa ga gungu uku, “Al-Maqsam” din shine IBAD(wato bayi) ba Al-Musdafaun ba,AL-MUSDAFAUN “qism” ne daga cikin “aqsam” na IBAD wanda yake shine AL-MAQSAM AR=RA’ISIY.AL-IBAD YANQASIMUN ba AL-MUSDAFAUN YANQASIMUN ba,ba zababbun ne suke karkasuwa ba,bayin ne suke karkasuwa ya zuwa ga zababbu da ba su ba.
Ba kuma gadarwan ce ba take karkasuwa ba,ba kuma su zababbun ne suke karkasuwa ba.Ita gadarwan an kebance ta ne kawai da zababbu daga cikinsu bayin,ee,haka ne,su zababbun anyi ta’arifinsu a cikin ayan akan cewa sashe na bayin,su AL-MUSDAFAUN din sashe na bayin.Wasu daga cikin bayin mu “zalim”,wasu daga cikn bayin mu “muqtasid”,wasu daga cikn bayin mu “saabiq” wa’yanda suke sune AL-MUSDAFAUN,wato ASSAABIQ shine AL-MUSDAFA daga cikin IBAD.MIN din LIT TAB’ID wato MIN din an kawo ta ne saboda “kaso”ba domin bayani ba.
Kuma abinda yake nuni zuwa cewa wannan gadarwan gadarwa ce ta AL-ILMUN LADUNNI na gaibu shine wannan ambaton da aka yi da SAABIQUN BIL KHAIRAT wato wanda ya rigaya daga cikin bayinmu akwai wanda ya rigaya da alherai,domin ASSABIQ a suratul waqi’a an yi ta’arifinshi da AL-MUQARRAB inda Allah yake cewa:
“WASSABIQUNAS SABIQUN ULA’IKAL MUQARRABUN”
Kuma shi AL-MUQARRAB anyi ta’arifinshi a suratul mudaffifin da cewa shi yana shedan ayyuka da kuma littafin nagari daga cikin bayin Allah,saboda Al-Kur’ani sashinshi ne yake fassara sashinshi,sashinshi yake gasgata sashinshi,ba ka daukan sashi komabayan sashi kayi tsammanin zaka fahimce shi.Allah yana cewa:
  “KALLA INNA KITABAL ABRARI LAFI ILLIYIN WAMA ADRAKA MA ILLIYUN KITABUN MARQUM YASH’HADUHUL MUQARRABUN.”
Saboda haka ASSABIQU a wannan ayan shine wanda aka kusanto dashi,kuma shine mai yin sheda akan aikin “abrar”,saboda haka shi yana “haimana” akan matsayin ILLIYIN wanda AL-ILLIYUN din shine wanda a cikinshi ake rubuta littafin “abrar”a wani littafi wanda ake ma numba “ay marqum”,wato wanda ake numba daya,biyu,uku.
In ka fahimci wa’yannan haqa’iq din a wani zango daban,Allah yasa ka fahimta.Sai muje mataki na gaba wanda yake cewa daya daga cikin mutane wa’yanda suke tsammanin zasu iya siffata A’immah (as) musamman Imam Ali,suna kokari su siffatasu din amma basu suke siffatawa ba,kila ma suna siffata akasinsu,kila ma suyi kuskure,kila ma suyi laifi a cikin “tausifin” su musamman mawaka.Mawakan bege da yabo da sauransu.
Yanayi ya sani a wa’yannan ‘yan kwanakin,na saurari wasu daga cikin wakoki na sha’irai masu yawa a babin bege da yabo,musamman bege da yabon Ahlul-Bait (as),daga sha’iran Shi’a da Sunnah.Kuma abinda zan yi yanzu kana iya ce mashi “AN-NAQD AL-AQA’IDIY AS-SARI’IL AABIR” akan wasu daga baituka kadan da wa’yannan sha’iran suke yi ba tare da neman irshadi ba a lokacin da suke wakokinsu din.
Amma naqadi “mufassal”,wannan jalasosi ne masu yawa,misali;Malam Mustapha Umar Baba Gadon Kaya yana cewa a lokacin da yake kirga falolin Imam Ali (as),yana cewa:
  “A gaban Khadija ya tasu Ummul Mu’umin”,ya kirga shi daga cikin fada’il na Ali(as),cewa a gaban Khadija Ali (as) ya taso Ummul Mu’umin,sai suka ce mashi “Babul ilimi”wato amshin kenan.
Kalla summa alfu kalla,bai taso a gaban Khadija ba (as),a gaban Annabi ya taso.Ba mu da nassi ingantacce wanda ya tabbatar mana cewa Ali(as) tarbiyan Khadija ne,ko akwai?Khadija ba zata iya tarbiyan Ali(as) ba,wanda yayi tarbiyyan Ali shine Manzon Allah (sawa).Muka ce maka Imam Ali (as) tun yana karami da hukuncin Allah Subhanahu wa Ta’ala Manzon Allah(sawa) ya dauko shi daga wajen hannun mahaifinshi Abu Talib,tun kafin Manzanci,ya kasance yana bibiyanshi akan dukkan abubuwan da ya kasance yana aikatawa,har daga karshe ya zama cewa ya gaje shi amma a wannan baitin sai yake cewa “a gaban Khadija….”yana kirga shi daga cikin fada’il da falaloli na Imam Ali da kuma cikin dalilan da suka sanya yafi kowa ilimi alhalin wakan yana cewa ne “Imam Ali shine kofa zuwa ilimin Manzon Allah”
Amma a lokaci guda kuma sai yake nuna cewa a gaban Khadija ya taso.Malam Mustapha Umar Baba G/Kaya haziki ne a cikin sha’iran Ahlul-Bait (as) “fil jumla” la “bil jumla”,in ka dauke shi “ka kul” nake su in ce,in ka dauke shi gabaki daya,ba baiti baiti jumla jumla a abubuwan da yake fadi ba.
Akwai cigaba…


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky