GAGGARUMIN BUKIN IDIN GHADEER A KADUNA

 GAGGARUMIN BUKIN IDIN GHADEER A KADUNA

Mu’assasar Thaqafar Thaqalayn Kaduna karkashin jagorancin Shugaban mu’assasar,wato Sheikh Hamzah Muhammad Lawal,ta yi gaggarumin taro domin murnar zagayowar ranar Ghadeer a dakin taro na gidan tarihin Arewa dake Kaduna jiya Lahadi 10 ga watan Agustus.

An fara taron ne da bude shi da addu’a daga Malam Abubakar Tofa,sai karatun Alkur’ani mai girma daga Malam Adam Musa,sannan sai aka mika abin magana ga Sheikh Hamzah Muhammad Lawal domin gabatar da darasi na musamman dangane da ranar ta Ghadeer.
Shehin malamin yayi ishara akan cewa kaman yanda ya fadi a shekaran da ta gabata cewa ko da ba nassi daga Allah Ta’ala ko kuma daga Manzonshi (sawa),idan aka maka “ardin” “Curriculum Vitae” na Ali (as),sannan aka maka “ardin” na sauran Sahabban Manzon Allah (sawa) aka ce maka a cikinsu ka zabi wanda kake ganin ya cancanci ya gaji Manzon Allah(sawa) da muhimma din tsayawa da addini?ya kamata ka zabi Ali(as).
Saboda Curriculum Vitae na Ali (as) ya fi na dukkan Sahabbai ba tare da ta’assubanci ba,ba tare da siyasa ba,ba tare da tamazhubi zuwa ga wata mazhaba ta tunani ko ta aqida ba.
Malamin ya cigaba da cewa kari akan wannan dangane da inzazozi na Imam Ali akwai nassosi sarihai,sannan akwai isharori da talwihohi daga Manzon Allah (sawa) tun farkon da’awa da risala har zuwa karshenta daga gare shi yana ankarar da mutane akan cewa su bi Imam Ali(as) a bayanshi.
A lokacin da Malamin yake bayanin yanda hajji daya tilo kuma na karshe da Manzon Allah yayi a rayuwarshi ya kasance, yana cewa:
  “Manzon Allah(sawa) hajji daya yayi a rayuwarshi  ta risala,sannan wannan hajjin shine wanda ya faro shi daga fitowa daga Madina a 24 ko 25 ko 26 ko 23 ga watan Zul-Qa’ada shekara ta goma bayan hijira wadda a wannan shekarar,kuma a wannan yinin Manzon Allah (sawa) ya fara haraka dinshi daga Madina din domin ya je Hajji.Wannan hajji shi ake ce ma;Hijjatul Islam ko Hijjatul Balag ko Hijjatul Kamal ko Hijjatut tamam.Dukkansu saboda da dalilai bayyananu kuma yankakku ake kiransu da wa’yannan sunayen.
“Manzon Allah (sawa) shi yayi wazana kuma yayi izini ma dukkan Sahabbai akan cewa su fito su bumbumta zuwa hajji-kaman irin kiran Ibrahim (as).Saboda haka ya zama dukkan mutanen gidanshi gabaki dayansu da matanshi zuwa Ahlulbait dinshi Alaihimus Salam duka sun fito tare dashi.Sannan Sahabbai masu yawan gaske wadanda ake kimanta adadinsu da alkalumma daban daban su ma suka fito;akwai alkamin da yake cewa 90,000,akwai wanda yake cewa 100,000,akwai wanda yake cewa 120,000,akwai wanda yake cewa 124,000 da sauransu.Kuma wa’yannan alkalumman suna ta’abiri ne akan wa’yanda suka fito dashi (Manzon Allah) daga Madina,basa ta’abiri akan wa’yanda suka fito daga sauran nahiyoyi da tawagoginsu wa’yanda suka cimma Manzon Allah(sawa) ko akan hanya ko kuma bayan ya shiga Al-Makkatul Mukarramah.
  “Kaman tawaqar Imam Ali wanda shine ma’abucin munasaba wadda ta taho daga Yamen da bisashe wa’yanda shi Ali Alaihis Salam ya taho dasu daga Yamen da tawaga,ko dashi da Abu Musa ko abinda yayi kama da wannan.Sannan da sauran tawagogi wa’yanda suka taho daga wasu wurare wanda wannan zai inganta mana mu ce:wa’yanda suka hajjanci wannan shekarar adadinsu babu wanda ya sani sai Allah Subhanahu wa Ta’ala.”
Bayan malamin ya bayyana abubuwa da suka dinga faru a kan hanyan Manzon Allah na zuwa hajjin wannan shekarar,da yanda Manzon Allah ya tsananta wajen koyawa wa’yanda yake tare dasu karantarwan  addini a lokacin,har zuwa kammala aikin hajji.Yayi bayanin abubuwan da suka faru a ranar Ghadeer yana cewa:
  “A lokacin da zo aka Ghadeer Khum,a wuraren Juhfa,wanda wannan wajen mararraba ne ko mahada ko matattara,a ranar Alhamis ko Juma’a,wato an yi kwanaki uku bayan hajji yanzu ana so a koma.A wannan wurin wanda yake Sahara ne sai Manzon Allah (sawa) ya tsaya-Dab’an,ya kamata in fadi akan cewa a wannan shekarar an yi kaman kyenda ko karambau saboda haka duk da wasu sun so su fito su biyo shi daga Madina amma basu iya ba saboda wannan karanbau din da ya shafi da yawa daga cikin mutane,saboda haka su basu yi hajji a wannan shekarar ba tare da Manzon Allah(sawa).
  “To,lokacin ya zo daidai wurin a Sahara,kowa zai san inda ya nufa,to,shine sai Manzon Allah (sawa) ya tsaya kafin mutane su rarrabu kowa ya zuwa ga nahiyar da ya fito,in daga Misr ya fito ya tafi,in daga Iraq ne ya tafi Iraq,in daga Yamen yake ya je Yamen,in daga ko’ina yake ya je.Sai Manzon Allah ya sauka ya yada zango a wani wuri wanda yake wurin ba ruwa ba ciyawa sai garjin rana sai zufa.Saboda haka sai musulmi suka yi mamakin saukarshi a wannan wurin wanda ba wani daga bayanshi wanda ya taba zama a wajen ya zama zango,shi akan kanshi bai taba sauka a wurin ba.Da ba don a ce wahayi yayi mashi magana ba da lahjan da yake bai saba jin irin wannan lahjan ba daga wahayi a da ba.
  “Allah Subhanahu wa Ta’ala yana ce mashi;Ya kai wannan Manzo-yana magana da shi biz zat-ka isar da wannan abin wanda aka saukar maka daga Ubangijinka,kuma in baka aikata ba,to,baka isar da sakon shi ba,kuma Allah zai kare ka daga mutane-wato zai tsare ka zai kare daga mutane.Sai da Allah ya bashi dukkan damanat sai ya isar da sakon.Wato sai da Allah ya bashi “divine guarantee”,akwai abin da ake ce ma “sovereign guarantee” wadanda shugabannin kasashe suke badawa.Shi wancan guarantee “was divine”.Shi ma “sovereign” ne,don Allah ne “sovereign” na haqaqa.Divine guarantee din shine “wallahu ya’asimuka minan nas”.
  “Sai ya zama (Manzon Allah) ba zai iya kara taki ba,ya tsaya a wurin kowa ya tsaya.Wato bai da makawa dole ya tsaya a wurin musamman saboda Allah ya bashi lamuni…..Abinda ake ce ma Addauha shine itaciya mai lema.Sai yasa aka  yi mashi mimbari na siradda sannan yasa aka yi abinda zai kare su,aka yi addauhat masu yawa kaman yanda Zaid Ibn Arqam ya rawaito,kaman yanda Ibn Kasir ya kawo a cikin Al-Bidaya wan Nihaya dinshi.
  “Manzon Allah (sawa) da yasa aka yi mashi wa’yannan dauhat din,sai ya tsaya tsakanin wa’yannan mutanen yace masu yaku mutane kaman an kira ni kuma na riga na amsa kiran………….Ni mai bari ne a cikinku nauyaya guda biyu;littafin Allah da itra dina wato Ahlulbait dina-bai bari wasu su yi mashi fassara ba,sai yace da itra dina wato mutanen gidana-saboda haka kuyi tsokaci ku duba ku hankalta akan yanda zaku yi mu’amala dasu a bayana,saboda su biyun ba zasu taba rabuwa har sai sun gangaro akaina a tafki a lahira.
  “Sannan sai yace;Hakika Allah Subhanahu wa Ta’ala shine maulana kuma nine waliyyin kowane mu’umini da mu’umina-zai fara shimfa,zai karrara,bayani ne jiddan mandilqi Manzon Allah ya taho dashi na dora hujja akan wa’yanda yake magana akansu,ba majal na rashin fahimta-…sai ya rike hannun Ali (as) yace wanda na kasance maulanshi (sharadi),to,wannan Alin maulanshi ne–wato wanda na rike hannunshi,ba sauran Ali Ali ba-Allah ka jibanci wanda ya jibance shi,kayi gaba da wanda yayi da shi(wannan muna karanta AlBidaya wan Nihaya).
  “Ibn Kasir ya kara akan cewa wanda ya rawaito hadisin daga Zaid Ibn Arqam yace ma Zaid din shin da kunnenka ka ji daga Manzon Allah?wato kaine ka ji mubasharatan ka naqalto daga Manzon Allah ko da wasida?da ta’abiri na malaman usulul hadis.Sai Zaid yace babu wani wanda ya kasance a cikin wa’yannan dauhat din face sai da ya ganshi da idanunsa guda biyu sannan ya ji da kunnuwanshi ko mutum nawa ne.
Malamin karanta hadisai masu yawa wadanda suka afku a wannan rana ta ghadeer din,da yanda Annabi ya sanya mutane suka dinga zuwa suna yi wa Imam Ali bai’a a wannan rana.
A lokacin da Malamin yake bayanin ma’anar kalmar “maula” ya kafa hujja da Sibd Ibn Jauzi daga malaman Ahlus Sunnah wanda ya dauki ma’ana ta goma ya watsar da sauran taran daga cikin ma’anonin kalmar “maula” wadda take nufin “aula”.
Sannan ya kara da cewa idan akwai abinda ya wuce haddin tawatur,to,wannan hadisin “man kuntu maulahu….” shine saboda yawaitan wadanda suka rawaito shi.A wannan wajen ya kawo maganar At-Tabariy dangane da hadisin,da ya rasa yanda soki hadisin sai yace ;“Haza la yufidush shi’a” wato wannan hadisin baya amfanar ‘yan shi’a.
Malamin ya tabo janibobi masu yawa a cikin jawabansa;yayi magana akan rundunar Usama da rashin lafiyar Manzon Allah na karshe da abubuwan da suka faru na umaurtan sahabbai da suka kawo warqa da abin rubutu.
Taron ya samu halartan mutane daban daban daga wurare masu yawa,sannan an kammala shi lafiya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky