DALILAI NA SIYASA SUKA SANYA AKA HANA RUBUTA HADISI DA DAWWANI SHI Inji Sheikh Hamzah Muhammad Lawal

DALILAI NA SIYASA SUKA SANYA AKA HANA RUBUTA HADISI DA DAWWANI SHI   Inji Sheikh Hamzah Muhammad Lawal

A cigaba da karatun Al-Milalu wan Nihal da Sheikh Hamzah Muhammad Lawal yake gabatarwa domin bayanin akidun Shi’a a kowace ranar juma’a a makarantarsa dake PRP Unguwan Sanusi Kaduna,ya bayyana cewa dalilai na siyasa ne suka sanya aka hana “tahdith” da “tadwin” a farkon musulunci.

Ya bayyana cewa babban dalilin da ya sanya aka hana hadisi da dawwana shi shine domin a boye fifiko da cancantar Ahlulbait a cikin al’umma domin ka da wata rana mutane suce yaya aka yi haka bayan sune suka fi cancanta da jagoranci?
Ya karfafi wannan da’awa ta shi da wani hadisi da yake bayanin ziyarar Sulaiman Ibn AbdulMalik zuwa hajj .Yana cewa:
  “Sulaiman Ibn AbdulMalik ya je hajji sai ya bi ta Madina,sannan sai ya dinga zuwa Mashahid din Manzon Allah(Sawa) wa’yanda yayi sallah a cikinsu da sauransu.Sannan sai ya umurci Abban Ibn Usman akan cewa ya rubuta mashi sirorin Annabi Sallallahu alaihi wa Alihi wa sallam,da kuma yake yakenshi wa’yanda yayi ya halarta,wato ya rubuta mashi record din wannan.
  “Sai Abban yace mashi( wato Sulaiman Ibn Abdulmalik daga cikin sarakunan Banu Umayya):Ina da ita rubutatta,na karbe ta ne a gyare daga wanda na aminta dashi,an riga anyi tahririnta an gyara.Saboda haka sai (Sulaiman Ibn Abdulmalik din) yayi umurni akan a yi kofin ita sira din da take hannun Abban.Ya ba marubuta guda goma kowa yayi kofi daya wato yayi nuska (wato za a yi nuska guda goma kenan).
  “Sai suka rubuta a fatu.To,lokacin da littafan suka kai gare shi(wato Sulaiman Ibn Abdulmalik),sai ya fara bincike ya fara karantawa,sai ya ga ba komai a ciki sai ambaton Al-Ansar a “aqaba” guda biyu (wato aqaba ta farko da ta biyu),da kuma ambaton Ansar a Badar –yanda suka taimaki Manzon Allah(sawa) a yakin Badar bayan Manzon Allah yayi hijara zuwa Madina.Sai (Sulaiman Ibn AbdulMalik) yace ;da ban kasance ina ganin wa’yannan mutanen (wato Al-Ansar) suna da falalar ba,wato ashe haka suke?
  “Ko dai ya zama mutanen gidana (wato Banu Umayyah) sun rufe wa’yannan falalolin ya zama mutane basu san su ba ko kuma ya zama asasan ba haka suke ba an kanbama su ne.Sai Abban Ibn Usman yace: Ya kai wannan Amir (wato Sarki),duk abinda suka aikata ba zai hana mu mu fadi gaskiya ba,yanda muka siffata su a wannan littafin haka suke.Yace duk da yake muna da sabani da su amma dole mu fadi gaskiya muyi adalci,wannan abinda muka rubuta haka ya faru a hakika,wato hakika muke bada labari,haka Ansar suke.Amma zuciyar Ibn Abdulmalik din ta kasa tahummuli -saboda tun asali mun fada maku abinda ya sanya Banu Umayya suke gaba.Cewa in za a fadi tarihin addinin musulunci babu su a ciki,su abinda za a ambata a cikinsu shine yakar Musulunci suka yi.Wannan kowa da kowa ya sani Umar dan Khattab ya fadi ba wai Ali Ibn Abi Talib ko Al-Hassan ko Al-Hussan ko sauransu ba.
  “Umar dan Kattab ya fadi akan cewa Mu’awiya dan Abi Sufyan bai da kaso a cikin shugabancin musulmi.A lokacin da muke baku labarin Ubada da yanda Umar dan Khattab ya goyi bayan Ubada akan Mu’awiyya da sauransu-
  “Sai shi Sulaiman Ibn Abdulmalik yake cewa:bana ganin ya kamata in cigaba da yin kofi na nuskokin wannan,sai na koma na fada ma Amirul Mu’uminin (wato mahaifinshi kenan) kila zai saba-in yace wannan siran ban amsa ba sai a canja ta-yanzu zan dauka in kaiwa mahaifi na(wato Abdulmalik Ibn Marwan) in ga mai zai ce dangane da abinda aka rubuta a ciki.
  “Sai ya bada umurni da a kona littafin,sai aka kona shi.Sai yace:zan tambayi shugaban muminai in na koma,in ya yarda a yi,ba abinda ya fi sauki a sake kofin shi,saboda haka dan an kona shi ba komai tun da ai akwai asalin,wato in yace;a’a,abinda na tafi akanshi ba haka bane,to,da cikin sauki za a sake amma ni yanzu ban yarda ba,sai ya kona ya kekketa shi.
  “Sai Sulaiman Ibn Abdulmalik ya koma daga hajji zuwa Sham bayan an gama hajji,sai ya ba mahaifinshi labari dangane da abinda ya kasance na ra’ayin Abban da sirar da suka rubuta wadda ta cika da ambaton falalolin Ansar,ba Banu Umayyah.To,sai shi Abdulmalik din mahaifin Sulaiman sai yace :Me ya same ka?Mecece bugatar ka akan cewa ka gabatar da littafi wanda a cikinshi babu falala gare mu?Kana so kai yanzu ka sanar da mutanen Sham al’amuran da ba so muke su sani ba?
  “To,sai Sulaiman yake cewa ai don haka ne ma ya sanya aka kona wanda aka min kofin shi  tun da-wato ashe ma na dace a ra’ayi kenan,ai shi yasa na aikata abinda na aikata tun Madina din har sai na san ra’ayin ka tukuna.Sai Abdlmalik din ya gasgata ra’ayin danshi din Sulaiman yace abinda ka yi daidai ne,kada a rubuta wannan sira din.
Malamin yace za a samu wannan riwayan da ya kawo a cikin “Al-Muwaffayat” na Zubair Ibn Bakkar ta hanyar wasidan yake yaken Manzon Allah (sawa),a shafi na 28.
Malamin ya kara da cewa in ya zama cewa ba zasu iya tahammulin fadin falalolin Ansar ba,to, ya kake tsammanin zasu iya tahammulin fadin falalolin Ahlulbait (as) wanda sun fi falalolin Ansar bil kasir?Ko falalolin Shugaban Ahlul bait din wato Ali dan Abi Talib?
Ya kara da  kawo wata riwaya wadda aka rawaito daga Khalid Al-Qusari wanda daya ne daga cikin masu riwayan Bani Umayyah cewa ya bugaci wani da cikin masu  rubuta mashi sira da ya rubuta mashi sira,sai shi mai rubutawan yace;ka fa sani in zan rubuta sira wani abu zai zo min na daga siran Imam Ali (as),in na zo wurin in rubuta?Sai Khalid ya bashi amsa da a’a,sai fa in da zaka ganshi a daben jahannama,wato in sharri ne ka rabuta.
Malamin yace za a samu wannan riwayan a cikin littafin Al-Agani,juzu’I na 22,shafi na 27 ga masu son su duba.
Masu sha’awan sauraron cikakken karatun suna iya neman karatun Al-Milal wan Nihal na shehin Malamin zama na 138


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky