DAGA RANAR DA AKA KAWO MIN RIWAYA KWAYA DAYA DA ISNADI TABBATACCE CEWA IMAM ALI YACE DUK WANDA YACE NA FI SAYYIDINA ABUBAKAR A Y

DAGA RANAR DA AKA KAWO MIN RIWAYA KWAYA DAYA DA ISNADI TABBATACCE CEWA IMAM ALI YACE DUK WANDA YACE NA FI SAYYIDINA ABUBAKAR A Y

DAGA RANAR DA AKA KAWO MIN RIWAYA KWAYA DAYA DA ISNADI TABBATACCE CEWA IMAM ALI YACE DUK WANDA YACE NA FI SAYYIDINA ABUBAKAR A YI MASA BULALA HADDIN IFTIRA’I, TO, DAGA WANNAN RANAR ZAN KOMA IZALA

---- Cewar Sheikh AbdulJabbar Sheikh Nasiru Kabara


A cigaba da karatun littafin Al-Ababeel wanda Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya gabatar a ranar Lahadi, 24/6/2018, a Masallacin Jami’ur Rasul dake birnin Kano, Sheikh Abduljabbar ya bayyana cewa daga ranar da aka kawo mai riwaya kwaya daya da isnadi tabbatacce cewa Imam Ali yace duk wanda yace na fi Sayyidina Abubakar a yi mashi bulala haddin iftira’I daga ranar zan koma IZALA.

Shehin Malamin yace:

“ Iyaka abinda masu fadi suke fada in kace Imam Ali ya fi Sayyidina Abubakar a ma bulala haddin muftari, kaman yanda Ibn Hajar ya kawo cikin Assawa’ikul Muhrika cewa Imam Ali yace duk wanda yace na fi Sayyidina Abubakar kuyi masa bulala haddin iftira’I, kuyi masa bulalar haddi ta iftira’i. Cewa Imam Ali ya fi Abubakar bulalan haddin wanda yayi karya ga musulmi. To, meye hujjar wannan maganar? Shi dai bai kawo isnadi ba duk da Ibn Taimiyyah a nan gun zai ce sama da gu tamanin amma bai isa ya kawo maka gu daya ba tabbatacce. Yana cikin karerayin da zan kawo nan gaba.

 “ Cewa Imam Ali wannan a sama da gu tamanin, ni kuma ina cewa wanda ya kawo ta da isnadi kwaya daya tabbatacce ba tamanin ba, daga rana iri daya da isnadi daya wanda ya inganta wanda yace wanda duk yace na fi Abubakar kuyi mai bulala haddin iftira’I ranar zan koma IZALA. Da isnadi daya ba tamanin ba, daya tal tabbatacce kan Sayyidina Ali ya fadi wannan.

 “ Ni ban yarda fa gina addini da karerayi ba. Cewa an ginu a kai sai suyi ta ginuwa su suka jiwo. Dan jama’a sun hadu a kan karya sai ta zama gaske? Karya ga malami da jahili duk sunan su karya, daya ce, hukuncinsu daya gun Allah. Da malami yayi karya da Jahili yayi karya duk daya ne sunansu karya. Babu wani ya jama’a da ya bambamta maganar malamai da na jahilai illa hujja. Ba wai don suna nada rawani ko sunansu Shehu ko malam wane ba, a’a, idan maganar malami ta ginu ba hujja da ita da ta kowane cikon gari day ace. Idan maganan Malami ta saba da waki’I karya sunanta, ko shine malam wa karya yake saidai a girmama shi saboda malami ne a ce ya fadi ba daidai ba a saya amma dai karya yake yi komi girmansa kuwa. To, y azan zo in yi addini da karya? Ka fadi maganar nan na bi babu ko na bi ba haka take ba, don kai ne malam wane ko masu fadanta na da yawa? A’a ba zan yi addini haka ba, domin addini ba wasa bane.”


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky