Alakar yan Shi'a da hukumomin kasashan su a mahangar Imamai ( a. s) da malaman shi'a :

Alakar yan Shi'a da hukumomin kasashan su a mahangar Imamai ( a. s) da malaman shi'a :

Muttaqa Tahir maradi ya rubuta!


مقدمة :
Daga cikin abinda ya wajaba akan duk wani mumini : kada yayi  wata magana ko wani aiki da ya shafi Aqida ko rayuwa,sai in ya dogara akan dalili - da ake la'akari dashi a shari'a-.

Daga cikin abinda ayau akafi yawan tsegumi akan shi : minene hukuncin mu'amala ko kuma aiki a karkashin hukumomin da ba na Musulunci ba ?

Anan ba Muna mukamin bada fatawa bane, abinda muke nufin mu ankarar da mutane shine : muguji yin hukunci daka, ya kamata mu rungumi bincike da karatu akan duk wani abu da bamu sani ba..

Idan mutum ya lura da rayuwar Imaman Shi'a da magan ganun su, zai same su kashi biyu :
1- maganan su da suke hana mabiyan su mu'amala da azzalumai da nufin taimaka masu akan zaluncin su.
2- maganan su-da kuma siran su- da suke halastawa mabiyan su aiki tare da azzalumai idan hakan zai kawo gara da kuma kare gaskiya da taimaka ma bayin Allah muminai..

Idan mutum ya koma ya Karanta rayuwar Imam Ali ( a. s)  zai kai ga wannan hakikar : Imam ( a. s)  Ya tabbatar -  a cikin magan ganun shi cewa : Khalifancin wanda suka gabace shi bai inganta ba, hakkin shine aka kwace :

لقد تقمصها إبن أبي قحافة وإنه ليعلم أن محلي منها محل القطب من الرحى!
Da sauran magan ganun shi da yake nuna : Khalifanci hakkin shi ne wanda babu mai jayayya dashi akan hakan.

Amma duk da haka, Imam Ali ( a. s)  bai gajiya ba wajan baiwa Khalifofin shawara akan abinda yake ganin kariya ne ga addini da Al'umma.
Umar dan khattabi ya sha fada cewa : ba dan Ali ba, da umar ya hallaka.
Hakanan Imam Ali ( a. s) Ya kasance yana cema mabiyan shi :
إذا إقترح عليكم منصبا فاقبلوه.
Idan aka maku tayin wani matsayi,- a zamanin Khalifofi- ku karba!

Hakanan kada mu manta cewa : akwai wani bawan Allah da ake kira : Aliyu bin yaktin علي بن يقطين
Ya kasance daga cikin mabiya Al'imamul sadiq da Al'ummul kazim ( a. s).  Ya karbi matsayin waziri a fadar Haruna Rashid da umarnin Imam musal kazim ( a. s). Wanda zaman shi a fadar Haruna Rashid ya taimaka sosai wajan taimakon shi'anci da yan Shi'a da kare rayukan su da dukiyoyin su.

Duk da kuma a gefe guda zaka samu wani lokaci, su Imaman ( a. s)  sukan hana wasu mabiyan su aiki, ko kusantar azzalumai! Kenan mi zamu iya fahimta anan?

Anan zamu iya gane cewa : ma'auni a mu'amala ko aiki tare da hukumomin da ba na Musulunci ba,- ko kuma aiki tare azzalumai- shine :

1- ya haramta idan har zai zama taimako ga azzalumi akan zaluncin shi.

2- ya halitta idan hakan zai taimaka wajan kare gaskiya da kare muminai.

الشيخ المظفر
Mai Aqa'idul Imamiyya ya kawo duka fuskokin guda biyu yana cewa :
عقيدتنا في الوظيفة في الدولة الظالمة :
إذا كان معاونة الظالمين ولو بشق تمرة بل حب بقائهم، من أشد ما حذر عنه الأئمة عليهم السلام، فما حال الإشتراك معهم في الحكم و الدخول في وظائفهم و ولاياتهم...  والمنغمسين في تشييد حكمهم؟ ( و ذلك أن ولاية الجائر دروس الحق كله، و إحياء الباطل كله و إظهار الظلم والجور و الفساد) كما جاء... عن الصادق عليه السلام.
Yana cewa : idan ya kasance taimakon azzalumai koda da dan guntun dabino ko san wanzuwar su, yana daga mafi tsananin abinda Imamai ( a. s)  suka tsoratar game da shi, to ya kaga halin mutumin da yayi musharaka tare dasu cikin hukuncin su da shiga cikin Ayyukan su... Da wanda sukayi nitso cikin karfafa hukuncin su ?...

Bayan ya kawo wannan fuskan, to kuma sai ya kawo fuskan ta biyo yana cewa :
غير أنه ورد عنهم عليهم السلام جواز ولاية الجائر إذا كان فيها صيانة العدل و إقامة حدود الله، والإحسان إلى المؤمنين، و الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر...
Duk da yazo daga gare su ( a. s) : ya halitta kar ban matsayi a karkashin azzalumi idan hakan zai zama - hanyar - tsaida adalci da tsaida dokoki, da kyautata ma muminai...

Kuma yace : a karkashin hakan akwai hadisai da yawa !

Saboda haka a duk lokacin da muminai suka shakhasa cewa : shiga cikin aiki tare da wanda wata gwamnati da ba ta Musulunci ba, idan har hakan zai kawo gara- ta wata fuska- to ba abinda zai hana suyi hakan.

Idan muka dawo muka duba mas'alan a mahangar fatawoyin manyan malamai, zamu iya ganin Al'amarin a fili.

Al'imamul Khomeini ( R.H) yana fada a cikin tahrirul wasila :
معونة الظالمين في ظلمهم بل في كل محرم حرام بلا إشكال...
 Taimakama Azzalumai a cikin zaluncin su, haramun ne bila ishkal...

و أما معونتهم في غير المحرمات فالظاهر جوازها مالم يعد من أعوانهم و حواشيهم و المنسوبين إليهم...  ولم يكن ذلك موجبا لازدياد شوكتهم و قوتهم.
Amma taimaka masu a cikin abubuwan da basu haramta ba, à zahiri ya halitta matuqar ba'a lissafa mutum cikin mataimakan su ba... Kuma hakan ba zai karfafasu ba - a cikin zaluncin su-.

Hakanan an Tanbayi Al'imamul khamna'i a cikin أجوبة :
العمل في الدولة الظالمة
س 272 : هل يجوز العمل بوظيفة في حكومة غير إسلامية؟
ج: يدور مدار جواز الوظيفة في نفسها.
Shin ya halitta ayi aiki cikin hukumar da ba ta Musulunci ba ?
ج :
 Hakan yana yana komawa zuwa shi kanshi aikin -  ya halitta a asli ko bai halitta ba-

س 273 : شخص يعمل في إدارة المرور في دولة غير إسلامية... فهل هذا العمل جائز؟  وما حكم الراتب الذي يأخذه إزاء عمله من الدولة؟
Mutum ne yana aiki a ma aikatar dake kula da kai kawon ababan hawa a wata kasa ta larabawa, kuma shike sa hannu akan takaddun mutanan dake sabawa dokokin kai kawon ababan hawa dan sakasu a kurkuku...shin wannan aikin ya halitta? Minene hukuncin karban kudin biya akan wannan aikin a cikin wannan daular?
ج : مقررات نظام المجتمع ولو كانت من دولة غير إسلامية، تجب مراعاتها على كل حال، و أخذ الراتب في قبال عمل حلال لا بأس به.
Dokokin tsarin mulkin - kasashe - koda kuwa kasar bata Musulunci bace, Wajibjne a kiyaye su a kowane hali, kuma karban biya- a wannan kasar-akan wani aiki na halal, ba yada matsala.

س 274 : بعد حصول المسلم على الجنسية (الأمريكية أو الكندية)  هل يجوز له أن يدخل في الجيش أو الشرطة؟ و هل يجوز له أن يعمل في الدوائر الحكومية...
Mutum ne ya samu nationalité- takardar zama dan kasa a America ko Canada, shin ya halitta ya shiga aikin soja ko dan sanda ?  Shin ya halitta yayi aikin office  a karkashin hukumar kasar?
ج: إذا لم يترتب على ذلك مفسدة ولم يستلزم فعل محرم ولا ترك واجب، فلا مانع منه.
Idan babu wata barna a cikin hakan, kuma hakan bazai sa aikata haram ba ko barin wajibi,  ba abinda zai hana ayi.

الخاتمة :
Don haka ya kamata mu gane cewa : shi'anci ba shine sabawa da wata gwamnati ba ko yin dai dai da ita. Shi'anci sakone kuma tsari ne daga Allah daga manzo daga Imaman tsira ( a. s). wannan sakon ba doli bane sai yayi dai dai da wata gwamnati kuma doli bane ya saba Mata. Shi'anci baya bin wani mutum, A'a !  Mutun ne doli yabi shi.
Manufar dan shi'a ba shine sabawa da wata gwamnati ba doli ko kuma yin dai dai da ita, manuf dan shi'a shine : yayi dai dai.

Yin aiki ko mu'amala da wata hukuma da bata Musulunci ba, ya halitta matuqar hakan zai taimaka wajan taimakon gaskiya da muminai.. Kuma kaine zaka tantance hakan da kanka.    Saboda kamar yadda malamai suke fada :
تشخيص الموضوع بيد المكلف
Tantance maudu'i yana hannun mukallafi!

 Allah yasa mu dace..

اللهم صل على محمد وآل محمد وعجل فرجهم

المصادر : سيرة الأئمة عليهم السلام : مهدي البيشوائي، ج 1 ص 404 - 411.
مكاتيب الأئمة : الشيخ علي الأحمدي الميانجي، ج 4 ص 470
تحرير الوسيلة :"الإمام الخميني قدس سره الشريف، ج1 كتاب المكاسب و المتاجر / المكاسب المحرمة و آداب التجارة.  / المسألة 14
عقائد الإمامية : الشيخ المظفر ص 114
أجوبة الاستفتاءات ج 1 : السيد القائد علي الخامنئي مد ظله، باب العمل في الدولة الظالمة.
ط / الدار الإسلامية
بيروت -  لبنان.
***********************


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky