Turkiya zata dauki hayar sama da sabbin jami'an soji 40,000

Turkiya zata dauki hayar sama da sabbin jami'an soji 40,000

Rundunar sojin Turkiya ta ce cikin wannan shekara ta 2018, zata dauki hayar akalla sabbin jami’ai dubu 43,000.

Matakin wanda kamfanin dillancin labaran kasar na Anadolu ya rawaito, ya zo ne bayanda gwamnatin Recep Tayyib Erdogan ta kori dubban ma’aikatanta, sakamakon zarginsu da hannu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a watan Yulin shekarar 2016.

Turkiya na zargin malamin Addini Fethullah Gulen wanda ke gudun hijira a Amurka, cewa shi ne ya kitsa yunkurin juyin mulkin, zargin da malamin ya ke ci gaba da musantawa.

Sama da mutane 300 ne suka rasa rayukansu yayin arrangamar da aka yi tsakanin jami’an tsaro masu biyayya ga gwamnati da kuma wadanda suka yunkurin juyin mulkin.

Tun daga lokacin ne gwamnatin Turkiya ta kori dubban ma’aikatanta daga aiki, ciki har da rundunar soji da kuma sauran ma’aikatun kasar, yayinda aka garkame da dama a gidan yari.

Turkiya ta kare kanta da cewa, ta dauki matakan ne tsaurara domin kawar da baki dayan magoya bayan Fethullah Gulen daga dukkanin ma’aikatun kasar.

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky