Zarif: Amurka Ba Zata Sake Yi Wa Iran mulkin Da Babakere Ba

 Zarif: Amurka Ba Zata Sake Yi Wa Iran mulkin Da Babakere Ba

Yayin da yake ishara kan goyon bayan Amurka na juyin mulkin da aka yiwa gwamnatin Muhamad Musadak a shekarar 1953, Ministan harakokin wajen kasar Iran Muhamad Jawad Zarif ya bayyana cewa ko yau Amurka na bayan yiwa Kasar Iran juyin mulki da zagon kasa , amma ba za ta taba cimma manufarta har abada ba.

Zarif ya ce a ranar 28 ga watan Mordad shekarar 1332 hijira shamsiya, shekaru 65 da suka gabata, Amurka ta yiwa zabbabiyar gwamnatin Muhamad Musadiq juyin mulki, tare da dora gwamnatin kama karya, inda al'ummar Iran suka kasance cikin kangi mulkin shiga-shugula da katsalandan na tsahon shekaru 25, a yau ma Amurka na kokarin sake maido da wannan mulkin  ta hanyan amfani da wani gungu, matsin tattalin arziki, watsa labaran karya na yaudarar al'ummar Iran, kuma har abada magabatan Amurkan ba za su cimma wannan bakar manufa ta su ba.

A makon da ya gabata ne, ma'aikatar harakokin wajen Amurka ta sanar da kafa wata kungiya domin karin matsin lamba a kan jamhoriyar musulinci ta Iran.

Ministan harakokin wajen Amurka ya ce za mu iya kokarinmu wajen yiwa gwamnatin Iran matsin lamba ta ko wani bangare.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky