Yarjejeniyar Nukiliya: Martanin Iran Da Tarayyar Turai Ga Shugaban Kasar Amurka

Yarjejeniyar Nukiliya: Martanin Iran Da Tarayyar Turai Ga Shugaban Kasar Amurka

A yau alhamis ne ake ganawa a tsakanin ministan harkokin Wajen Iran da takwarorinsa na turai, domin jaddada riko da yarjejeniyar Nukiliya

Ganawar ta yau tana a matsayin maida martani ne ga shugaban kasar Amurka Donald Trump wanda yake shirin bayyana sabon matsayinsa akan yarjejeniyar da kakabawa Iran wasu sabbin takunkumai.

Jami'a mai kula da harkokin wajen tarayyar turai Federica Mogherini ta yi kira da kada a shigar da batun yarjejeniyar Nukiliya a cikin sauran abubuwan da ake da sabani da Iran akan su.

Kasashen turai dai suna ganin cewa wajibi ne su hada kai domin kare yarjejeniyar wacce aka cimmawa a 2015, bayan tsawon lokacin da aka dauka ana tattaunawa.

Nan da wasu kwanaki ne ake sa ran shugaban kasar na Amurka zai bayyana matsayarsa akan yarjejeniyar Nukiliyar da kuma batun takunkumi akan Iran.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky