Tarayyar Turai Bazata Dorawa Iran Takunkumi Ba

Tarayyar Turai  Bazata Dorawa Iran Takunkumi Ba

Kwamishinan ayyukan noma da kuma raya karkara na tarayyar Turai Mr Phil Hogan ya bayyana cewa ba wata kasa a cikin tarayyar turai da take da tunanin dorawa Iran takunkumi idan Amurka ta yi watsi da yerjejeniyar da ta kulla da ita.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Phil Hogan yana fadar haka a wata hira da ta hada shi na kwamishinan a jiya Asabar. 

Jami'in na tarayyar Turai ya kara da cewa idan gwamnatin Amurka ta yi watsi da yerjejeniyar shirin makamashin nukliya da ta kulla da Iran, tarayyar Turai ba zata goya mata baya wajen maida takunkuman da aka dorawa Iran a baya ba. Kuma babu wata kasa daga cikin kasashen Turai take da wannan tunanin a halin yanzu.

Phil Hogan ya kara da cewa a wannan shekara tarayyar Turai ta kulla yerjejenita ta bunkasa ayyukan noma da JMI wanda kimansa ya kai Euro Miliyon 10.

A jiya Asabar ne Phil Hogan ya jagoranci wata tawagar tarayyar Turai wacce ta kunshi yan kasuwa 70 zuwa nan birnin Tehran.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky