Shugaba Rohani Zai Halaci Taro A Turkiyya

Shugaba Rohani Zai Halaci Taro A Turkiyya

Shugaban kasar Iran ya kama hanyar tafiya zuwa kasar Turkiyya domin halattar zaman taron kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta O.I.C kan matsalar Palasdinu.

Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdugan ne ya kirayi zaman taron gaggawa na shugabannin kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta O.I.C domin tattauna batun hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da kai wa kan al'ummar Palasdinu musamman batun kisan kiyashi da ta yi wa Palasdinawa a yankin Zirin Gaza a ranar bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Qudus.

Ana sa-ran shugabannin kasashen Musulmi fiye da 40 ne zasu halacci zaman taron gaggawan da za a gudanar a yau Juma'a a birnin Istambul na kasar ta Turkiyya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky