Qasimi: Ya Kamata Bin Salman Ya Dauki Darasi Daga 'Yan Kama Karya Da Suka Gabace Shi

Qasimi: Ya Kamata Bin Salman Ya Dauki Darasi Daga 'Yan Kama Karya Da Suka Gabace Shi

A martanin da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya mayar wa yarima mai jiran gado na masarautar Al Saud, ya bayyana cewa yana da kyau Bin Salman ya dauki darasi daga 'yan kama karya da suka gabace shi.

Muhammad Bin Salam yarima mai jiran gado na Saudiyya, a wata zantawa da ya yi da jaridar New York Times ta kasar Amurka, ya yi maganganu na batunci a kan Iran da kuma jagoran juyin juya halin muslunci na Iran, tare da bayyana hakan a matsayin salon sabuwar siyasar masarautar tasu.

Bahram Qasimi ya ce duk da cewa yarima yaro ne matashi da ke cikin kuruciya saboda karancin shekaru, da kuma rashin masaniya kan lamurra da suka shafi siyasar duniya, amma zai fi dacewa da shi ya binciki tarihin sarakuna da shugabannin kama karya da aka yi a yankin gabas ta tsakiya da yadda suka bauta ma Amurka da yahudawa, da kuma yadda karshensu ya kasance.

Ya ce wata kila idan yarima ya zauna ya yi karantun ta natsu, mai yiwuwa a nan gaba ya dawo cikin hankalinsa.

Qasimi ya kara cewa, sakamakon matsalolin da yariman ya haifar a cikin gidan sarautarsu a  halin yanzu tsakaninsa da sauran 'ya'yan gdan sarautar, da kuma shigar shugular da ya yi kan lamarin Lebanon tare da tilasta firayi ministan kasar yin murabus, ya sanya masu hankali a duniya ba sa bayar da muhimmanci ga maganganunsa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky