Ministan Tsaron Iran: Za Mu Ci Gaba Da Karfafa Makamanmu Masu Linzami Don Mayar Da Martani Ga Makiya

Ministan Tsaron Iran: Za Mu Ci Gaba Da Karfafa Makamanmu Masu Linzami Don Mayar Da Martani Ga Makiya

Sabon Ministan tsarkon kasar Iran Birgediya Janar Amir Hatami ya bayyana cewar ma'aikatar tsaron kasar za ta ci gaba da karfafa karfin makaman da take da shi ta yadda babu wani makiyin da zai yi tunanin kawo wa Iran hari, yana mai cewa ya kamata makiya su san cewa duk wani kokarin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci gagarumin mayar da martani mai kaushin gaske.

Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya bayyana cewar ministan tsaron ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da tashar talabijin na kasar Iran a daren jiya inda ya ce siyasar tsaron kasar Iran ita ce karfafa kai da sanya makiya jin cewa ba za su sha ba matukar gigi ya debe su suka kawo wa kasar Iran hari. A saboda haka matukar dai wani gigi ya debe su suka kawo wa Iran hari, to kuwa za su debi kashinsu a hannu.

Janar Hatami ya kara da cewa: Karfafa karfin kare kai shi ne babban abin da muka sa a gaba, don haka za mu yi amfani da dukkanin karfin da muke da shi wajen cimma wannan manufa, yana mai sake jaddada shirin ma'aikatar tasa na kara karfafa irin karfin da Iran take da shi a fagen makamai masu linzami.

Cikin shekarun baya-bayan nan dai Iran ta kera makamai masu linzami masu cin gajere, matsakaici da kuma dogon zango don kare kanta daga duk wata barazana ta makiya lamarin da ke ci gaba da daga hankulan makiya musamman Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky