Ministan Harkokin Wajen Kasar Faransa Ya Fara Ziyarar Aiki A Tehran

Ministan Harkokin Wajen Kasar Faransa Ya Fara Ziyarar Aiki A Tehran

Ministan harkokin wajen kasar Faransa tare da tawagarsa sun iso birnin Tehran a safiyar yau Litinin don hudanar da ziyarar aikin ta kwanaki 2.

Kamfanin dillancin Labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa kafin zuwan sa Bahram Qasimi kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ya bayyana cewa Jean-Yves Le Drian zai gana da shugaba Dr Hassan Ruhuna da kuma tokoransa Mohammad Javad Zarif, inda ake saran bangarorin biyu zasu tattauna batutuwan da suka hada kyuatta dangartakar da ke kasashen biyu, harkokin tsaro a yankin gabas ta tsakiya da kuma na kasa da kasa. 

Kafafen yada labaran kasar Faransa dai sun bayyana cewa, ziyarar da Jean-Yves Le Drian ya fara a nan Tehran, ta sharar fage ce ga ziyarar da shugaban kasar Emmanuel Macron zai kawo nan Tehran nan ba da dadewa ba.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky