Miliyoyin Iraniyawa Ne Suka Domin Nuna Goyon Bayansu Ga Tsarin Musulunci

Miliyoyin Iraniyawa Ne Suka Domin Nuna  Goyon Bayansu Ga Tsarin Musulunci

Miliyoyin Iraniyawa a duk fadin kasar sun fito kan tituna don tunawa da ranar 30 ga watan Disamban shekara ta 2009, a lokacin da suka dakile shirin manyan kasashen duniya na kawo tashin hankali a kasar don kuma kawo karshen tsarin musulunci a kasar .

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto cewa a jiya 30 ga watan disamba  ana gudanar da gangami a birane daban daban don tunawa da wannan ranar, a lokacin da suka jaddada goyon bayansu ga tsarin musulunci wanda yake jagorancin kasar da kuma shugabancin waliyul faqih.

A lokacin dai rikici ya tashi ne bayan da yan takarar shugabancin kasar biyu, wato Karubi da Mir Husain Musawi wadanda basu sami nasara a zaben da aka gudanar a cikin watan yuli na shekarar ba suka tara magoya bayansu wadanda suka fara kone-kone da lalata kayayyakin gwamnati, har'ila da kashe jami'an tsaron kasar.

A lokacin ne kasashen yamma suka ruruta wutar tashe tashen hankulan wanda ya dauki kwanaki ana ta yi. Amma a lokacin da miliyoyin mutane suke fito don nuna goyon bayansu ga tsarin musulunci sai fitinar ta zo karshe.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky