Limamin Juma'a Na Iran Ya Bayyana Masu Hannu A Rikicin Iran

Limamin Juma'a Na Iran Ya Bayyana Masu Hannu A Rikicin Iran

Limamin da ya jagoranci sallar juma'a ta nan birnin Tehran ya ce hatsaniyar da ta faru ne a nan kasar Iran shiri na babban Shaidan Amurka da Haramcecciyar kasar Isra'ila tare da taimakon kudi na masarautar Saudiya

Hujjatu-Islam wal Musulimin Kazim Siddiqi cikin hudubarsa ta sallar juma'a ya bayyana cewa hatsaniya da kuma fitinar da ta kuno kai a cikin 'yan kwanakin nan ya fitar da hakikanin fuskar kungiyar 'yan ta'adda munafikai da makiyan al'ummar  kasar Iran, kuma shakka babu al'umma kasar sun ware kansu daga masu kokarin tayar da fitina da hatsaniya a kasar.

Daga ranar 28 ga watan Dicembar 2017 din da ta gabata ce, wasu daga cikin al'ummar kasar suka fara gudanar da tarurruka gami da zanga-zangar neman sauki a rayuwa, ganin yadda kayayyakin masrufi ke kara hauhawa a kasar, inda wasu 'yan tsiraru suka yi amfani da wannan dama wajen tayar da hatsaniya bisa goyon bayan wasu kasashen waje a kasar.

A yayin da yake ishara kan rawan da wasu kasashen waje suka taka a game da wannan hatsaniya, Limamin da ya jagoranci sallar juma'a na birnin Tehran ya ce har zuwa lokacin da al'ummar kasar Iran ta kiyaye 'yancinta  kuma ta tsaya wajen kalubalantar fice gona da iri na kasashe masu girman kai, to za su nasara a kan duk harin da za a kawo wa kasar.

Hujjatu-Islam wal Musulimin Kazim Siddiqi ya tabbatar da cewa  ya zuwa yanzu Al'ummar kasar Iran sun dakile makirce makircen makiya, kuma fagen gwagwarya da suka nushi bakin Amurka da haramcecciyar kasar Iran gami da kawayensu masu neman rikici da tayar da hankula a Duniya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky