Jami'an Tsaron Kan Iyaka Na Kasar Iran 8 Ne Suka Yi Shahada A Fafatawa Da Yan Ta'adda A Yammacin Kasar

Jami'an Tsaron Kan Iyaka Na Kasar Iran 8 Ne Suka Yi Shahada A Fafatawa Da Yan Ta'adda A Yammacin Kasar

Majiyar ofishin gwamnan lardin Azarbaijan ta yamma a kasar Iran ta bada sanarwan shahadar jami'an tsaron kan iyakar kasar 8 a jiya Juma'a a fafatawar da suka shiga da yan ta'addan a kan iyakar kasar da kasar Turkiya

kamfanin dillancin Labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto mataimakin gwamnan lardin Azarbajan ta yamma Ali-Rida Rodfar yana fadar haka a jiya juma'a, ya kuma kara da cewa an fafata ne tsakanin jami'an tsaro da 'yan ta'adda a kan iyakar kasar da Turkiya, inda aka halaka adadi mai yawa na 'yan ta'addan, yayin da 8 daga cikin jami'an tsaron suka yi shahada.

Labarin ya kara da cewa yan ta'addan 'yan kungiyar Pajok ce wacce kungiyar PKK ta kurdawan kasar Turkiya suka kafa tare da taimakon wasu kasashen yamma don samar da tashe-tashen hankula a yankin. Rahoton ya ce kasashen Amurka, Britania da kuma HKI suna daga cikin wadanda suke tallafa wa wannan kungiyar. Kuma ko a ranar 28 ga watan Mayun da ya gabata 'ya'yan wannan kungiyar sun fafata da jami'an tsaron kasar Iran a birnin Arumiyeh babban birnin  lardin Azarbajan ta yamma inda a lokacin ma jami'an tsaron kan iyakar kasar 2 suka yi shahada.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky