Iran Na Kara Karfin Sojojin Kasanta

Iran Na Kara Karfin Sojojin Kasanta

Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Aya. Sayyid Aliyul Khaminae ya ce babu alamun za'a yi yaki tsakanin Iran da makiyanta a nan kusa, amma dole sojojin kasar su kasance cikin yanayin ko da kwana, sannan sun karfafa kansu don fuskantar makiya a ko yauce.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehrai ta nakalto jagoran yana fadar haka a jiya Lahadi a lokacin da yake ganawa da jami'an rundunar sojojin sama na kasar da ke nan birnin Tehran, wato rundunar Khatam al-Anbiya . Ya kuma kara da cewa shirin ko ta kwana da zasu yi yana matsayin ibada ne don dukkan ayyukansu don neman yardar Allah ne.

Ya ce rundunonin sojojin sama a ko yauce su ne a gaba a duk lokacinda aka fara yaki, don haka akwai muhimanci ya kasance suna cikin shiri a ko wani lokaci.

Kafin jawabin jagoran komandan rundunar sojojin sama na Khatam al-Anbiya  Brigadier General Alireza Sabahifard ya gabatar da rahoto dangane da rundunar tasa da kuma irin shiriye-shiryen da take yi a halin yanzu da kuma na gaba.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky