Iran: Daliban Jami'o'i Sun Yin Zanga-zangar Tir Da Kisan Musulmin Rohingya

Iran: Daliban Jami'o'i Sun Yin Zanga-zangar Tir Da Kisan Musulmin Rohingya

Daliban sun yi cincirindo a bakin ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Tehran suna masu tir da shirun da duniya ta yi akan kisan na musulmin Rohingya.

Bugu da kari daliban jami'o'in sun soki halin fuska biyu na Majalisar Dinkin Duniya akan ayyukan ta'addanci da suke faruwa a duniya. Bayanin da suka karanta ya kunshi nuni da harin ta'addancin da aka kai a birnin Paris a 2015 wanda duniya ta yi tir da shi, amma kuma duniyar ta yi shiru akan hare-haren da ake kai wa a Yemen da kuma Mayanmar.

Har ila yau masu Zanga-zangar sun bayyana gwamnatin Mayanmar a matsayin mai aikata manyan laifuka, sannan kuma suka yi tir da shirun da kasashen musulmi suka yi musamman ma dai na larabawan yankin tekun pasha.

Tun a ranar 25 ga watan Augusata ne dai  sojojin gwamnatin kasar Mayanmar suka fara kai hare-hare akan musulmin Rohingya a yaniin Rakhine wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka da kuma tilastawa wasu 300,000 yin hijira daga gidajensu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky