IAEA: Iran Tana Ci Gaba Da Yin Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya

IAEA: Iran Tana Ci Gaba Da Yin Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya

A zaman da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta gudanar a jiya, ta sake jaddada cewa cewa har yanzu Iran tana ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tsakaninta da manyan kasashen duniya.

A lokacin da yake gabatar da nasa jawabin a jiya a gaban babban taron hukumar na shekara-shekara wanda aka gudanar a jiya a birnin Vienna na kasar Austria a karo na 62, shugaban hukumar ta IAEA Yukiya Amano ya kara jaddada cewa, bisa dogaro da dukkanin rahotanni da hukumar ta tattara, har yanzu Iran ba ta saba ko daya daga cikin abubuwan da yarjejeniyar nukiliya da aka cimamwa tare da ita ta kunsa ba.

Wannan rahoto na hukumar IAEA na a matsayin babban martani ga shugaban kasar Amurka Donald Trump, wanda ya fice daga wannan yarjejeniya bisa hujjar cewa Iran tana gudanar da shirinta a boye, kuma yarjejeniyar da aka cimmawa da ita tana da nakasu.

A nasa bangaren shugaban hukumar makamshin nukiliya ta kasar Iran Dr. Ali Akbar Salehi, ya bayyana ficewar da Amurka ta yi daga wannan yarjejeniya a matsayin lamari mai matukar hadari, kuma a cewarsa hakan yin fatali ne da dokoki da ka'idoji da kuma tsare-tsare na majalisar dinkin duniya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky