Hukumar IAEA Ta Ce; Iran Tana Aiki Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Kan Shirinta Na Makamashin Nukiya

Hukumar IAEA Ta Ce; Iran Tana Aiki Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Kan Shirinta Na Makamashin Nukiya

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta fitar da rahoton cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana aiki da dukkanin yarjejeniyar da aka cimma kan shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya.

A rahoton da hukumar kula da makamashin nukiya ta duniya IAEA ta fitar a jiya Juma'a kan shirin Iran na makamashin nukiya yana dauke da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana aiki da dukkanin yarjejeniyar da aka cimma tsakaninta da hukumar kan shirinta na makamashin nukiya musamman a fagen tace sinadarin yuraniyom.

Rahoton ya fayyace cewa: A karkashin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasar Iran da bangaren manyan kasashen duniya biyar gami da kasar Jamus kan yawan sinadarin yuraniyom da Iran din zata tace, a halin yanzu haka kasar ta Iran tana tace kasa da yadda aka cimma yarjejeniya da ita.

Wannan shi ne farkon rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan shirin makamashin nukiyar kasar Iran tun bayan da Donald Trump ya dare kan karagar shugabancin Amurka kuma yake nuna adawarsa kan yarjejeniyar da aka cimma da kasar ta Iran.

Tun a shekara ta 2015 ne dai aka cimma yarjejeniya kan shirin makamashin nukiliyar Iran tsakaninta da manyan kasashen duniya biyar masu kujerar din din din a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya gami da kasar Jamus da ake musu lakabi da gungun kasashen 5+1 lamarin da ya kawo karshen takaddamar da ake yi kan shirin makamashin nukiliyar kasar ta Iran na zaman lafiya tare da dage mata tarin takunkumin zalunci da aka kakaba kanta.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky