Gwamnatin Kasar Iran Ta Shigar Da Karar Wasu Kafafen Yada Labai A Gaban Hukumar OFcom

Gwamnatin Kasar Iran Ta Shigar Da Karar Wasu Kafafen Yada Labai A Gaban Hukumar OFcom

Gwamnatin kasar Iran ta rubuta wasikar shigar da kara da kuma koke kan yadda wasu kafafen yada labarai a kasar Britania suke taimakawa masu tada fitina a kasar , ga hukumar kula da kafafen yada labarai na kasar Britania OFcon a takaice.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar diblomasia na kasar Iran a birnin London tana cewa jakadan Iran a London ne yan rubuta wasikar a madadin gwamnatin Jumhuriyar Musulunci ta Iran ga hukumar ta OFcom, inda a cikin wasikar ya ambaci wasu kafafen yada labaran na kasar musamman BBB farsi wacce take yada shirye-shiryenta da harshen farisanci suna kodaitar da masu tada fitana a wasu yankunan kasar da su yi amfani da makamai sun kuma tada hankali a kasar.

wasikar ya kammala da cewa wannan dabi'ar ta wadannan kafafen yada labarai ya sabawa aikin jarida na kwarewa a cikin kasar Britania ko kuma na kasa da kasa. .


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky