Fira Ministan Iraki Ya Kai Ziyarar Aiki A Tehran

 Fira Ministan Iraki Ya Kai Ziyarar Aiki A Tehran

Fira ministan na Iraki ya gana da shugaba Rauhani na Iran a birnin Tehran a yayin gudanar da ziyarar aikin

A yayin ganawar tasu shugaba Rauhani ya taya Haidar Abadi murnar nasarar da dakarun Iraki suka samu wajen karya lagon 'yan ta'adda a kasar, tare da bayyana wannan nasara ta dakarun Iraki da cewa nasara ce da dukkanin al'ummomin yankin gabas ta tsakiya suke murna da ita.

Rauhani ya jaddada goyon bayan Iran ga kudirin gwamnatin Iraki na ci gaba da zaman Iraki a matsayin kasa guda da al'umma guda, duk da banbancin addinai da mazhabobi da kuma kabilu.

A nasa bangaren Haidar Abadi ya yaba da irin goyon bayan da Iran take baiwa Irakia  dukkanin bangarori na siyasa, tattalin arziki da kuma tsaro, tare da jaddada cewa kasashen biyu masu tsohuwar alaka ta tarihi na dubban shekaru, za su ci gaba da kasancewa tare da juna.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky