An Gudanar Da Bukukuwan Ranar Haihuwar Imam Ridha a.s

An Gudanar Da Bukukuwan Ranar Haihuwar Imam Ridha a.s

An gudanar da bukukuwan ranar haihuwar Limami na 8 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Al..(s), wato Imam Aliyu bin Musa (a) a duk fadin Iran a daren jiya.

Dubban masu ziyara daga warare daban daban sun halarci hubbaren Imam Aliyu bin Musa (a) dake birnin Mashad da kuma na yar uwansa Fatima maasuma dake birnin Qum a jiya da dare inda suka karanta ziyarori da addu'o'i na musamman don zagayowan wannan ranar. Sannan mawaka sun yi ta rera wakokin yabon iyalan gidan manzon rahama masu tsari a wurare tarurruka daban daban a duk fadin kasar. 

An haifi Imam Aliyu bin Bin Musa (a) wanda akewa lakabi da Imam Rida a ranar 11 ga watan Zulkida shekara ta 148 a birnin Madina . Mahaifinsa Imam Musa bin Jaafar (a) ya yi shahada a shekara ta 183 wanda ya maida Imam Rida (a) jagoran al-ummar kakaknsu har zuwa shima shahadarsa a shekara ta 203 a birnin Maru na lardin khurasan kusa da birnin Mashad a nan Iran. Tsawon limamancin sa shekaru kimani 20, inda ya kasance a Madina na tsawon  shekaru 17 sauran shekaru ukku kuma a lardin Khurasan. 

Muna taya al-ummar musulmi musamman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) murnar zagayowan wannan ranar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky