Yemen: Sojojin Kasar Yemen sun sake kwace yankunan da su ke karkashin ikon 'yan koren Saudiyya.

Yemen: Sojojin Kasar Yemen sun sake kwace yankunan da su ke karkashin ikon 'yan koren Saudiyya.

A jiya alhamis ne sojojin kasar ta Yemen su ka kwace wani yanki da ke gundumar Ma'arib daga hannun 'yan koren Saudiyya.

A jiya alhamis ne sojojin kasar ta Yemen su ka kwace wani yanki da ke gundumar Ma'arib daga hannun 'yan koren Saudiyya.

Majiyar soja daga kasar ta Yemen ta ce; Sojoji da kuma dakarun sa-kai na Ansarullah, sun yi nasarar kwace iko da yankunan ali-Salim da al-khadi a yammacin gundumar Ma'arib da ke tsakiyar kasar.

Bugu da kari, majiyar sojan ta ci gaba da cewa; Sun yi nasarar rusa da lalata motocin soja biyu na sojojin Saudiyya a arewacin al-makha da ke gabar ruwan gundumar Ta'iz.

Fiye da mutane 10,000 ne Saudiyyar ta kashe a kasar Yemen, tunda ta shelanta yaki a cikin kasar.288

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky