'Yan Ta'addan IS Sun Rusa Masallacin Al-Nouri Da Hasumiyar Mosul

 'Yan Ta'addan IS Sun Rusa Masallacin Al-Nouri Da Hasumiyar Mosul

Rundunar sojojin Iraki ta fida sanarwa cewa; kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta wargaza masallacin Al-Nouri da kuma hasumiyar Mosul mai dadadden tarihi.

Fira ministan Iraki Haidar al'Abadi ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa wargaza wadanan wurare ya nuna cew an yi galaba ne ga yakin da ake da kungiyar IS.

Saidai a wata sanarwa data fitar ta hanyar shafin yada farfagandanta na amaq, kungiyar ta IS ta musunta wargaza wuraren tana mai dora alhakin hakan ga jiragen yakin Amurka.

Amman kawancen yaki da 'yan ta'addan na IS ya ce kungiyar ta wargaza daya daga cikin mayan wurare masu tarihi na Mosul da Iraki.

Idan ana tune a masallacin na Al-Nouri ne dake Mosul Abou Bakr al-Baghdadi ya ayyana kansa a matsayin Khafika bayan da kungiyar ta IS ta mamaye yankin a cikin shekara 2014.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky