Yan Ta'adda Sun Kai Hari Da Makami Mai Linzami Kan Ofishin Jakadancin Rasha Da Ke Kasar Siriya

Yan Ta'adda Sun Kai Hari Da Makami Mai Linzami Kan Ofishin Jakadancin Rasha Da Ke Kasar Siriya

Kungiyoyin 'yan ta'adda sun kaddamar da harin wuce gona da iri da makami mai linzami kan ofishin jakadancin kasar Rasha da ke birnin Damasqas fadar mulkin kasar Siriya a yau Laraba.

Rahotonni daga Siriya sun bayyana cewa: Gungun 'yan ta'addan kasa da kasa da aka jibge a kasar Siriya sun harba makami mai linzami daga nesa, inda suka yi nasarar samun ofishin jakadancin kasar Rasha da ke yankin Jubar a gefen birnin Damasqas fadar mulkin kasar Siriya a yau Laraba, sai dai harin bai janyo hasarar rai ba.

A bangare guda kuma jiragen saman yakin rundunar sojin Siriya sun yi luguden wuta kan sansanonin 'yan ta'addan kungiyar Da'ish a lardunan Riqqah, Diru-Zurr da suke arewa da kuma gabashin kasar Siriya a yau Laraba, inda suka kashe 'yan ta'adda da dama tare da rusa sansanoninsu.

Rahotonni sun bayyana cewa; A bayan kai hare-haren na yau, sojojin gwamnatin Siriya sun kutsa yankunan garuruwan na Riqqah da na Diru-Zurr da nufin tsarkake su daga samuwar 'yan ta'addan da suka rage.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky