Yahudawan Sahayoniyya 'Yan Kaka Gida Sun Killace Wani Yankin Masallacin Aksa

  • Lambar Labari†: 817436
  • Taska : Pars Today
Brief

Tsagerun yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida sun sake daukan matakin mamaye wani yankin Masallacin Aksa da ke birnin Qudus.

A ci gaba da keta hurumin Masallacin Aksa da ke birnin Qudus a Palasdinu, wasu gungun tsagerun yahudawan sahayoniyya da suke samun kariya daga sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun mamaye wani yanki na Masallacin Aksa daga bangaren kofar Almagharibah a safiyar yau Litinin.

A kokarin da suke yi na tunzura Palasdinawa; Tsegerun yahudawan sahayoniyyan sun dauki matakin mamaye bangaren Masallacin na Aksa ne da sunan gudanar da ayyukan ibadunsu a wajaje masu tsarki lamarin da ke kai ga bullar tarzoma a Masallacin na Aksa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky