Yahudawan HKI Zasu Hana Kiran Sallah A Dukkan Masallatai A Yankunan Palasdinawa

Yahudawan HKI Zasu Hana Kiran Sallah A Dukkan Masallatai A Yankunan Palasdinawa

Komitin da majalisar ministocin HKI ta kafa don hana kiran sallah a yankunan Palasdinawa da ta mamaye da su ya amine da dokar kuma mai yuwa cikin yan kwanaki masu zawa gwamnatin haramtacciyar kasar zata hana kiran salla a wadannan yankuna.

Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta ce komitin ne ya bayyana haka a jiya Lahadi bai kuma yi karin bayani ba. Amma sanrawan baya bayan nan ta nuna cewa dokar zata sake komawa majalisar Kenest wacce zata maida bukatar doka.

Dokar ta bukaci hana dukkan kuwace kuwace injita, a wadannan yankuna daga karfe 11na dare zuwa 7 na safe wanda zai hada har da sallar asubaha na musulmi. Da farko dai komitin ya fadada lokacin hana abinda suka kira kuwace kuwace daga yamma, sai suna gano cewa zau hada har da jiniyan da yahudawan suke kunnawa a yammacin ranar Jumma'a, don haka suka bukaci sauya dokar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky