Turkiyya Na Ci Gaba Da Aikewa Da Sojoji A Yankunan Kurdawan Siriya

Turkiyya Na Ci Gaba Da Aikewa Da Sojoji A Yankunan Kurdawan Siriya

A ci gaba da farmakin da take kaiwa a yankunan Kurdawan na Siriya, Turkiyya ta sake aikewa da wani ayarin motocin soji a yankin Anadan

Farmakin dai da Turkiyya ke kaiwa mai taken « Rameau d’olivier » tana kaisa ne kan magoya baya da mayakan dake fafatukar kare Kurdawa na (YPG) da Turkiyyar take dangantawa da 'yan ta'adda. 

Turkiyya dai na son mamaye yankin Afrin dake yankin Halep na Siriya, kafin ta doshi birnin Manjib.

Farmakin da Turkiyya ke kaiwa da manya makaman yaki iri daban daban na ci gaba da hadassa hasara rayuka da jikkata fararen hula.

Babban asibitin lardin Afrin dai ya bukaci kasashen duniya dasu kawo karshen hare-haren da Turkiyya ke kaiwa tare da gargadi akan irin bala'in da hakan zai haifar, duba da yadda harkokin kiwan lafiya ke kara tabarbarewa a yankin, baya ga karancin magunguna da aka soma fuskanta. 

Kamfanin dilancin labaran (ANHA) dake dasawa da Kurdawa Siriya ya ce kawo yanzu fararen hula 104 ne suka rasa rayukansu kana wasu 156 suka raunana tun soma hare haren da Turkiyyar ta kaddaram yau da kwanaki 13.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky