Tsohon Shugaban Kasar Masar Zai Fuskanci Daurin Shekara Uku A Gidan Yari

 Tsohon Shugaban Kasar Masar Zai Fuskanci Daurin Shekara Uku A Gidan Yari

Wata kotu a Masar ta yanke hukuncin daurin shekaru uku a gidan kurkuku kan tsohon shugaban kasar Muhammad Morsi.

Kotu a kasar Masar a yau Asabar ta yanke hukuncin daurin shekaru uku a gidan kurkuku kan tsohon shugaban kasar Muhammad Morsi da wasu mutane 18 kan laifin cin mutuncin ma'aikatar shari'ar kasar.

Har ila yau kotun ta yanke hukuncin tara kan tsohon shugaban kasar, inda zai biya Alkali Muhammad Annimir kudin kasar Masar pound miliyan guda kan cin zarafinsa da ya yi ta hanyar bata masa suna a kafofin watsa labarai.

Tun a watan Yulin shekara ta 2013 ne sojojin suka kifar da gwamnatin Muhammad Morsi na kungiyar Ihwanul- Musulimin tare da tsare shi a gidan kurkuku kan zarge-zarge masu yawa da suka hada da cin amanar kasa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky