Sojojin Yamen Sun Yi Luguden Makamai Masu Linzami Kan Sojojin Hayar Saudiyya

Sojojin Yamen Sun Yi Luguden Makamai Masu Linzami Kan Sojojin Hayar Saudiyya

Sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun yi luguden makamai masu linzami kan sansanonin sojojin hayar masarautar Saudiyya tare da halaka sojojin masu yawa.

Majiyar rundunar sojin Yamen a yau Talata ta sanar da cewa: Sojojin Yamen da dakarun kungiyar Ansarullah sun yi luguden wuta da makamai masu linzami kan sansanin sojin hayar masarautar Saudiyya a yankin Karsh da ke lardin Lahij a kudancin kasar, inda harin ya yi sanadiyyar halakar sojojin da dama tare da jikkata wasu na daban.

Har ila yau sojojin na Yamen da dakarun sa-kan sun harba makaman masu linzami kirar "Zilzal 1" kan barikin sojin hayar masarautar Saudiyya mai suna al-Mo'azab da ke lardin Jizan a kudu maso yammacin kasar Saudiyya.

A gefe guda kuma jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai hare-haren wuce gona da iri har sau hudu kan yankin Zahir a lardin Sa'adah da ke arewacin kasar Yamen a yau Talata.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky