Sojojin Siriya Sun Fatattaki 'Yan Da'ish A Yankin Palmyra

Sojojin Siriya Sun Fatattaki 'Yan Da'ish A Yankin Palmyra

Hukumar dake sa ido kan al'amuran kare hakkin bil adama a Syria ta ce 'yan ta'addan Da'esh sun janye daga mafi yawancin yankin Palmyra.

Hukumar ta OSDH ta ce mayakan na IS ko Da'esh sun janye daga galibin yankin na Palmyra mai tarihi, bayan da suka dasa nakiyoyi a wurare da dama cikinsa.

Darectan hukumar, Rami Abdel Rahmane ya shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP cewa an yanzu haka 'yan kunar bakin wake na kungiyar ta IS sun doshi unguwanin dake gabashin birnin na Palmyra.

A jiya Laraba ne sojojin Syria dake samun goyan bayan takwarorinsu na Rasha suka samu shiga yankin na Palmyra bayan fatatakar da sukayiwa 'yan ta'addan na IS.

Saidai a cewar labarin nakiyoyin da mayakann na IS suka dasa a wurare da dama cikin yankin na zamen babban kalubale ga dakarun gwamnatin ta Syria.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky