Sojojin Gwamnatin Siriya Sun Kashe 'Yan Ta'adda Da Dama A Yankunan Kasar

Sojojin Gwamnatin Siriya Sun Kashe 'Yan Ta'adda Da Dama A Yankunan Kasar

Sojojin gwamnatin Siriya sun yi nasarar halaka 'yan ta'adda fiye da 150 a yankin Jubar da ke lardin Raqqa a shiyar arewacin kasar.

Majiyar tsaron Siriya ta sanar da cewa: A farmakin da sojojin gwamnatin Siriya suka kai ta sama da kasa kan yankunan da suke shiyar arewacin kasar musamman yankin Jubar da Ma'amal sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda fiye da 150 tare da tarwatsa motocin yakinsu.

Har ila yau dauki ba dadi tsakanin sojojin da 'yan ta'adda ya yi sanadiyyar jikkatan 'yan ta'adda da dama tare da tarwatsa wasu jerin motoci da aka makare su da bama-bamai.

Ayyukan ta'addanci sun kunno kai ne a kasar Siriya tun a shekara ta 2011 kuma kasashen Amurka da kawayenta na kasashen Larabawa musamman Saudiyya gami da Turkiyya su ke kara ruruta wutan ayyukan ta'addanci a kasar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky