Rundunar sojin kasar Lebanon ta bayyana samun nasarar kwace yanki na uku mafi muhimmanci da ke karkashin mayakan IS da ke arewa maso gabashin kan iyakarta da kasar Syria.
Tun a jiya ne, sojin Lebanon suka kaddamar da farmaki kan yankin Ras Baalbek, yankin kasar tilo da ya rage a karkashin mayakan IS, wadda ta mamaye tun a shekarar 2014.
Sojin kasar 10-ne suka jikkata, yayinda suka hallaka mayakan kungiyar ta IS guda ashirin.
Wani mazaunin kauyen na Ras Baalbek, ya ce sun yi matukar farincikin fatattakar mayakan da aka yi daga yankin.288