Saudiyya Ta Bude Iyakarta Da Qatar Saboda Aikin Hajji

Saudiyya Ta Bude Iyakarta Da Qatar Saboda Aikin Hajji

A wani abu da ake kallonsa a matsayin sassauci a rikici diflomatsiya na tsakanin kasahen Qatar da Saudiyya, sarki Salman ya bada umurnin bude iyakar kasashen biyu.

Wannan matakin dai a cewar kamfanin dilancin labaren Saudiyyar na SPA, domin baiwa mahajjatan kasar ta Qatar ne damar shiga kasar domin gudanar da aikin hajjin bana.

Rahotannin kuma sun ce hakan ya biyo bayan wata ganawa da yarima mai jiran gado na Saudiyyar  cewa da Mohammed ben Salmane ya yi da wakilin Doha Sheikh Abdallah ben Ali Al Thani a cikin daren jiya a Jeddah.

Babu dai wani abu da yake nuna cewa ko matakin na da nasaba da warware rikicin diflomatsiyya na tsakanin kasashen biyu, amman tuni masu sharhi suka bayyana cewa hakan wata alama da Saudiyya ke son nuna cewa bata saka siyasa a cikin harkokin aikin hajji.

A kwanan baya dai an yi ta zargin Saudiyya da sanya siyasa a cikin harkokin shirya aikin hajji.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky