Sabon Rikicin Syria Ya Raba Mutane 66,000 Da Muhallensu

Sabon Rikicin Syria Ya Raba Mutane 66,000 Da Muhallensu

Offishin kula da ayyukan jin kai na MDD, ya fitar da wani rahoto a yau dake cewa sabon rikici a Syria ya cilastawa mutane 66,000 kaura daga muhallensu a yankin Halep

Rahotanni na hukumar ta OCHA ya ce adadin ya hada har da na mazauna  Al'Bab inda mutane sama da 39,000 suka fice daga yankin.

Hukumar ta OCHA dai ta nuna damuwar ta dangane da halin da jama'ar ke ciki saboda nakiyoyi da abubhuwa masu hadari da 'yan ta'addan IS suka binne a yankunan.

Dama kafin hakan hukumar dake sa ido kan kare hakkin bil adama ta kasa a Syria (OSDH) ta ce sama da fararen hula 30,000 galibi mata da yara ne suka fice daga yankin a lokacin da dakarun Syria suka doshi yankin na Halep


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky